Tinubu ya gana da Sanata Shekarau a asirce

Daga BASHIR ISAH

Jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau inda suka yi ganawar sirri.

Kafin ganawar tasu, sai da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da takwaransa Abubakar Badaru na Jigawa suka ziyarci Kano inda suka nuna goyon bayansu ga ɓangaren Shekarau na jam’iyyar APC ƙarƙashin shugabancin Ahmadu Haruna Zago (Ɗanzago).

Sai dai babu wani cikakken bayani
a kan abin da Shekarau da Tinubu suka tattauna yayin ganawar tasu, amma rashin ganin Ganduje a wajen ganawar ya haifar da tambayoyi da dama masu neman jawabi.

Rikicin APC a Kano ya yi ƙamari ne tun bayan da aka gudanar da babban taron jam’iyyar na jihar a ranar 18 inda aka samu shugabannin jam’iyya guda biyu, ɗaya daga ɓangaren Gwamna Gandunje gudan kuma daga ɓangaren Sanata Shekarau.

Ɓangaren Shekarau ya zaɓi Haruna Ɗanzago ne a matsayin shugaban jam’iyya na jiha yayin da tsagin Ganduje ya ce shi Abdullahi Abbas ya sani a matsayin shugaban jam’iyya.

Daga bisani, kwamitin ƙoli na jam’iyyar ya ce shi ma Abdullahi Abbas ya sani a matsayin shugaban APC a Kano.

Rashin gamsuwa da matsayar kwamitin ƙolin ya sanya ɓangaren Shekarau garzayawa kotu tare da neman kotun ta sauke tarurrukan da ɓangaren hamayyarsa ya gudanar a matakin unguwanni da ƙananan hukumomi da kuma matakin jiha sannan ya tabbatar da nasa ɓangaren a matsayin mai nasara.

A ranar Talatar da ta gabata Babbar Kotun Abuja ta amince da buƙatar ɓangaren Shekarau, inda ta miƙa masa nasarar shugabancin jam’iyyar tasu sannan ta dakatar da ɓangaren Ganduje, tare da bai wa ɓangaren umarnin ko da wasa kada ya sake ya naɗa sabbin shugabannin jam’iyya.