Buhari ya rushe hukumomin kula da hada-hadar man fetur da shugabanninsu

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar litinin ɗin da ta gabata ne, dai gwamnatin tarayyar Najeriya, tare da sahalewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta tabbatar da rushe Hukumomin kula da hada-hadar man fetur, DPR da PPPRA da kuma PEP. wato dai ta shafe su tas!

Su Hukumomin kula da hada-hadar man fetur wani sashe ne na albarkatun man da yake da alhakin kula da farashi da kuma tattarawa tare da kasafta kuɗaɗen sashen albarkatun man fetur.

Ministan albarkatun man fetur na Najeriya, Cif Timipre Sylva, shi ya bayyana haka a yayin wani taro na ƙaddamar da kwamitocin kula da hada-hadar man a Abuja. Ministan ya ƙara da cewa, a yanzu haka ma dai, an rushe dukkan shugabannin hukumomin kula da hada-hadar man fetur ɗin na  DPR da PPPRA da kuma PEP.

Sai dai a cewar sa, aikin ta kan shugabannin hukumomin kaɗai ya biyo. Domin su sauran ma’aikatan hukumomin suna nan daram, ba a kore su ba, a cewar sa.

Timipre Sylva ya ƙara da cewa, bayan kawar da tsaffin shugabannin, shugaba Buhari a cikin hikimarsa bai ƙyale mazauninsu ba kowa ba.

Ya samar da kwamitoci da za su cigaba da aikinsu kuma ya naɗa waɗanda suka dace su shugabanci kwamitocin. Kuma a halin yanzu suna can suna dakon amincewar majalisa.

Kuma a cewarsa, yanzu ne Gwamnati za ta samu kwanciyar hankali gami da samun tabbacin cewa, hukumar tana wajen hannu nagari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *