Ko tashin gwauron zabin man fetur na duniya zai amfani Nijeriya?

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar juma’ar da ta gabata ne, aka sanar da farashi ma fi tsada da gangar man fetur ta yi. Abinda ya kai aka fara sayar da kowacce gangar mai a kan farashin Dalar Amurka Tamanin da biyar ($85) a kan kowacce ganga.

Abinda masana da masu bincike suka bayyana cewa, rabon da farashin ya yi tashin gwauron zabi kamar haka tun shekaru uku baya. Wato tun a watan  Oktobar shekarar 2018. Hasali ma dai, wannan shi ne karo na farko da farashin ya taɓa haura dalar ta Amurka tamanin ($80) in ji Kamfanin Brent oil, masu saita farashin mai na Duniya.

Mahukuntan harkar mai a garin Texas ta Arewa a ƙasar Amurka su ma sun ƙara da cewa, farashin ya ƙaru lokaci guda da kusan kaso ɗaya. Wato sifuli da ɗigo tamanin da biyar (0.85) a ranar juma’ar. Abinda wasu kuma suke ganin ƙarin kuɗin a matsayin buɗi ga masu safarar fitar da mai zuwa ƙasashen ƙetarensu. Wato kamar Nijeriya da take fitar da man.

Wannan tashin farashin ba ya rasa nasaba da ƙaruwar buƙatuwa da man fetur da ƙasashen Duniya suka yi. Inda suka matsa lamba ga ƙashen da suke samar da man fetur (OPEC) wanda Najeriya ma tana cikinsu, da ƙawayen burminsu da su haɓaka yawan  man da suke samarwa fiye da wanda suka saba samarwa a kowanne wata. Inda su kuma suka amince.

Amma abin tambayar, shin ƙarin farashin man yana da alfanu ga ƙasar Nijeriya? A ra’ayin wani masanin tattalin arziki, Simon Kolawole, ya bayyana cewa, Nijeriya a wajenta ƙarin kuɗi da rashinsa tamkar dai a ce juma da ɗan jummai. Ko a ce duk ɗaya, wai makafi sun yi dare. Domin ko da an ƙara ma, ba ta cin ribar komai.

A cewarsa, idan mai ya yi tsada, dole farashin kaya zai tashi a ƙasar. Kuma ƙasa ba za ta bar hakan ya afku ba. Dole za ta nemi mafita domin talaka ya samu sauƙi, ko da ta hanyar yin ƙundumbala ne. 

Hakazalika ta ɓangaren tallafin mai, komai tsadarsa dole Nijeriya ta yi amfani da wasu kuɗaɗen da ta samu musamman a ribar man da na harkar noma domin ta cikashe wa talaka ku]in tallafin mai domin kada sabon ƙarin farashin man ya shafe shi. Wato dai a cigaba da sayen sa a kan farashin  da ya saba. Ka ga an yi ba a yi ba.

Daga ɗarshe ya bayyana cewa, mafita ɗaya ta rage ga gwamnatin Nijeriya in dai har tana son shawo kan matsalar shi ne, ta hana fasa-ƙwaurin man fetur zuwa maƙwabtan ƙasashe kamar Kamaru da Benin da sauransu. Ko kuma ta cire tallafin mai, faƙat!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *