Buhari ya yi alhinin harin Sakkwato

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa game da mummunan harin baya-bayan nan da ‘yan fashin faji suka kai kan wasu matafiya a Jihar Sakkwato.

Cikin sanarwar da ta sami sa hannu Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Femi Adesina a ranar Laraba, Buhari ya ce, “Na yi matuƙar damuwa da yadda mutuwa ta cimma waɗannan ‘yan ƙasa yayin da suke kan hanyarsu ta tafiya zuwa wani sashe na ƙasa.

“Wannan ya nuna matsalar da wannan gwamnatin ke fuskanta wadda take buƙatar haɗin kan ‘yan Nijeriya ne don magance ta.

“Ina miƙa ta’aziyyata ga ahalin duka waɗanda harin ya rutsa da su, sannan ina bada tabbacin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da ƙokorinsu domin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan ta’addar.”

Idan dai za a iya tunanawa, MANHAJA ta rawaito yadda ‘yan fashin daji suka tare da kuma ƙona wasu matafiya a cikin motarsu a Sakkwato bayan da suka taso daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni a Talatar da ta gabata.