Numfashin mutum (5)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalamɗalaikum. Barkanmu mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan Adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikin ku ke aiki.

Zan ci gaba da bayani akan numfashin mutum cikin yardar Allah. A makonnin da suka shuɗe, na kawo bayanin yadda iskar oksijin ke shiga cikin jikin ɗan Adam. Sannan kuma a satin da ya wuce, na fara bada bayan yadda ake fitar da iskar kabon dai ogzayid daga jikin ɗan adam, ma’ana saga cikin huhu izuwa iskar duniya. Na tsaya a inda na ke cewa: 

  1. Fitar da Iskar Kabon Dai Ogzayid. Iskar da ta baro cikin huhu maras kyau wadda zata fita, ta kasance mai ɗumi da kuma danshi.  Yayin da ta zo hanci, sai waɗannan jijiyoyin jini su zuqe ɗumin, su busar da ita kafin ta fita waje. To kun ji asalin danshi da ɗumin da ake sanyawa busasshiyar iska wadda ta shiga cikin hanci daga duniyarmu. Amfanin ɗumama iskar da za ta shiga cikin huhun mu shi ne kiyaye hanyoyin iska, huhu, da kwayoyin halittun da suke taka rawa wajen numfashi daga bushewa da ƙandarewa, wanda hakan kan haifar da matsala.

Kasancewar hanci na dauke da ‘yan ƙananan hanyoyin jini masu yawa, ya sanya haɓo ya zama sanannen abu. Haɓo jini ne mai zuba daga jijiyoyin jinin da suke kusa da shamakin da ya raba hanci zuwa ƙofofin hanci guda biyu. Kuma haɓo kan iya faruwa a sanadiyyar naushi ko kutufo a hanci, ko bushewar wani sashe na kogon hanci, ko shigar ƙwayar cutukan jiki, da kuma matsalolin da suka shafi saurin daskarewar ko kamewar zubar jini wato “blood clotting”.

To daga kogon hanci, bayan da waɗancan abubuwa da suka faru tsakanin iska da kuma ƙananan jijiyoyin jini, sai iska ta shiga wata ‘turaka’, inda hanyar iska ta sadu da hanyar abinci, wadda ake kira da ‘pharynks’, daga nan kuma sai iskar ta zarce izuwa akwatun murya, wato inda ake samarwa da mutum murya. Akwatun murya an gina ta ne da guntsi, kuma a zaune take daram a bigirenta (a wuya) saboda tallafi da ta samu daga tsokokin nama, da kuma tantanin igiyoyin da ke kewaye da ita.  

Mafi bayyanar abin da zaka iya gani dangane da akwatun murya shi ne tsinin makwallato. Sai da iska mutum kan iya magana; kuma ana samar da sautin magana ne a cikin akwatun murya. Domin qarin bayani, sau ku dakaci rubutuna Wanda zan yi nan gaba kaɗan da yardar Allah.

Daga akwatun murya, iska sai ta shiga cikin bututun iska wato “trachea”. Wata iskar za ta shiga babban reshen bututun iska (main bronchus) na dama, wata kuma za ta shiga na hagu. Kar ku manta babban reshen bututun iska na dama shi ne ya shiga huhun dama, hakazalika na hagu, shi ya shiga cikin huhun hagu. Dukkan su sun ci gaba da yin rassa a cikin huhun, har su ƙare a matsayin ƙoƙon musayar iska.

Iskar oksijin za tayi ta bin waɗannan rassa har sai ta isa ƙoƙon musayar iska, inda anan ne ake musayar iska guda biyu: ta oksijin da ta kabon dai ogzayid. Musayar na faruwa ne tsakanin ƙoƙon musayar iska da kuma hanyoyin jinin da suke kewaye kowanne.

A nan ne iskar oksijin take barin asalin titin da ta shigo, wato ta tashi daga ƙoƙon musayar iska sannan ta tsallaka wani shamaki, kaana ta shiga cikin jini. Shi kuma jini sai ya ɗauke ta ya kakkaita sassan jiki, wato ƙwayoyin halittu, domin a yi amfani da ita.

Amma kafin iskar ta tsallaka daga ƙoƙon musayar iska izuwa cikin jini, sai ta ƙetare wani shaamaki mai rubi 6 wanda ake kira da “respiratory membrane”. Yana da matukar siranta kuma tantani ne wanda ƙwayoyin halittar da suke jikin bangon hanyar jini, da kuma wadanda suke jikin bangon “ƙoƙon musayar iska “suka samar da shi, wato damfarewar su da juna ne ya samar da wannan shamaki na “respiratory membrane “

Sirintakar wannan shamaki yasa iska bata shan wahala wajen ƙetare shi ta shiga cikin jini. Sai dai wasu dalilai sukan sanya ainihin siffar wannan shamaki ta sauya, musamman cututtukan da suka shafi huhu da ƙwayoyin halittarsa. Shan taba shima ya na kawo lalcewar wannan siffar ta wannan tantani; a dalilin haka, isasshiyar iska ba za ta samu ƙetarewa ba ballantana ta isa inda ake buƙata.

Saboda sirintakar wannan tantani, iskar oksijin tana ƙetara shi ne ta shiga cikin jini a gwargwadon lokaci na rabin sakwan! Wannan a lokacin da kake numfashi a kwanciyar hankali kenan. Amma a lokacin da mutum ke motsa jiki, ko ya razana, gwargwadon lokacin da iskar da take ɗauka kafin ta ƙetare zai iya kaiwa kwata na sakwan. Ya danganta da tsananin motsa jikin.

Yayin da iskar oksijin ta ƙetara ta shiga cikin jini, sai ta maƙale a jikin halittar da ke sanya jini ya zamto JA. Wannan shi ake kira “haemoglobin”. Shi yana a matsayin ‘motar’ ɗaukar iska ne, walau ta oksijin daga huhu zuwa ƙwayoyin halittu, ko ta kabon dai ogzayid daga ƙwayoyin halittu zuwa huhu; ya danganta da yanayi.
Da akwai matsaloli da dama da suke kawo cikas da zai hana maƙalewar iskar oksijin da wannan halitta wato ‘motar da ke ɗaukar iska’ jo “haemoglobin” a turance,  wanda hakan ke haifar da rashin lafiya. Saboda haka idan kin/ka tashi yau, kuna iya numfashi, kuma cikin ƙoshin lafiya, to godewa Sarkin halitta Wanda ya kiyaye ka daga afkuwar wadancan matsaloli.

A koda yaushe, ba sai kana aiki ba, ƙwayoyin halittar jikin mu suna buƙatar a kawo musu iskar oksijin, sannan a dauke musu iskar kabon dai ogzayid; numfashi ke taimakawa wajen tabbatar da faruwar hakan. Gwargwadon yawan iskar oksijin da tsokar jiki ke bukata a yayin da mutum baya komai yana kaiwa mil 250 a duk minti guda. A lokacin da yake mosta jikinsa kuwa, kwayoyin tsokar na bukatar iska mai yawan mil 4000 duk minti guda.

Akwai wani abun mamaki da ya shafi bayanin ƙoƙon musayar iska, wato, wanda na manta ban fada ba. Kamar yadda nace: siffar balan-balan (balloon) gare shi, kuma ana samun sa a cikin huhu gungu gungu, kamar dai ace ku sami nonon ayaba masu yawan gaske. Ƙaddara ayabar ita ce ƙoƙon musayar iskar, mariƙin nonon kuma—mashigar da ta tattare su waje guda.

An kiyasta yawan ƙoƙon musayar a cikin huhu ya kai miliyan 200 zuwa 300. To da za a tsaga kowanne, a ɓare shi, (kamar yadda idan an ɓare ɓawon gyada wasu lokutan, ɓawon saman kan maƙale a jikin ɗan uwansa), a ce bayan an tsaga su, kuma an ɓare su, an jere su waje guda, data kusa da ɗaya, a auna tsawon da fadin dukkanin ƙoƙon musayar iskar, to da za su yi daidai da girman filin ƙwallon kafa! Allah Buwayi!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *