Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Nda-Isaiah

Daga BASHIR ISAH

A ranar Alhamis da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya kai wa iyalan marigayi Nda-Isaiah ziyarar ta’aziyya dangane da rasuwar Mrs Eunice Ndanusa Nda-Isaiah wadda ta rasu a ranar 8 ga Afrilu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa, Marigayiya Eunice, ita ce mahaifiyar wanda ya kafa kamfanin Jaridar Leadership, wato marigayi Sam Nda-Isaiah.

Buhari wanda Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya wakilta ya ce, Gwamnatin Tarayya ta yi matuƙar alhini da rasuwar Mama Eunice.

Ya ce, a zahiri ana ganin kyawawan ayyukan da marigayiyar ta aiwatar a halin rayuwarta a wajen ‘ya’yanta ciki har da marigayi Sam Nda-Isaiah.

Ya ce, “Da so samu ne, da mun fi buƙatar Mama ta gabaci Sam tafiya gidan gaskiya, sai dai Allah cikin hikimarSa ya tsara komai ya auku kamar yadda Ya so.

“Kuma babu yadda za a yi mu zo wannan ta’aziyyar ba tare da tunawa da Sam Nda-Isaiah da kuma irin gudunmawar da ya bai wa ƙasa ba a halin rayuwarsa.”

Shugaba Buhari ya ce, rasuwar Sam da Mama Eunice ba zai sa gwmanati ta yanke zumuncin da ke tsakaninta da ahalin gidan ba.

Daga nan, ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayiyar, tare da cewa nasarorin da ta samu a halin rayuwarta za su ci gaba da yin tasiri a kan zuri’arta.

Da yake jawabi a madadin sauran dangi, Dr Tunde Owoyele ya nuna godiyarsu ga Shugaban Ƙasa da ya samu ikon turo tawagarsa don yi musu ta’aziyya.

Lai Mohammed ya jagoranci tawagar ne bisa rakiyar Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu, Dr Adaora Anyanwutaku da sauransu.

An haifi marigayiyar ne a tsohuwar Kabba da ke Arewacin Nijeriya, kuma bayan da ta yi girma ta yi zama wurare da suka haɗa da Kano, Kaduna da kuma Niger.

Fitaccen editan nan na jaridun New Nigeria da Triumph, Mr Clement Ndanusa-Isaiah, shi ne wanda ya auri marigayiyar a shekarar 1961.

Sunan “Maman Sam” da aka san ta da shi ya samo asali ne daga sunan ɗanta na farko, Sam Nda-Isaiah.