Yadda kifewar kwale-kwale ya yi ajalin mutane 26 a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mutane 26 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da ake ci gaba da neman wasu, bayan kifewar kwale-kwale a kogin Shagari da ke Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Shagari, Aliyu Ɗantani, wanda ya shaida haɗarin ga Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN, a Laraba a Sakkwato, ya ce lamarin ya faru ne a yammacin Talata.

Ɗantani ya ce daga cikin gawarwakin 26 da aka gano, 21 mata ne yayin da biyar kuma ƙananan yara, ya ƙara da cewa ana ci gaba da aikin ceto sauran fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen.

Shugaban ƙaramar hukumar, ya ce ba a iya tantance haƙiƙanin adadin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen ba.

A cewarsa, a halin yanzu dai masana kogi na cikin kogin don ganin yadda za a gano wasu gawarwaki ko kuma ceto waɗanda suka tsira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *