An cafke Ba’amurke ɗauke da bindigogi da alburusai a filin jirgin Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani Ba’amurke da ya shigo Nijeriya ɗauke da muggan bindogogi ya shiga hannun jami’an kula da bodar Nijeriya a filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed dake jihar Legas.

Shi dai wannan fasinja ya shigo ƙasar Nijeriya ne ta cikin wani jirgi wanda ya taho daga garin Houston na Amurka, inda jirginsu ya sauka a Nijeriya ƙarfe 10 da mintuna goma na safiya. 

Makaman da ya shigo da su sun haɗa da, muggan bindigogi guda biyu (babba da ƙarama) da tulin albirusai waɗanda ya vioye cikin hikima a  kayansa. 

Sannan kuma wannan Ba’amurken fasinja da aka ɓoye sunansa yana ɗauke ne da guda biyu; ɗaya na Amurka, ɗaya kuma na Nijeriya.  

Wata majiya daga filin jirgin na Murtala Muhammad dake Legas ta bayyana cewa, shi fasinjan ya voye waɗannan makamai ba tare da ya bayyana su ba a tashar binciken ba. 

Wata majiya kuma ta bayyana cewa, mutumin yana ɗauke da wasu takardu  waɗanda suke shaida cewa hukumar ƙasar Amurka ta bashi damar mallaka da ta’ammali da bindigogi. Amma kuma ba za a iya tantance ingancin takardun kai-tsaye ba. 

Majiyar ta ƙara da cewa, har ya zuwa lokacin haɗa wannnan rahoto, wannan ɗan Amurkan yana can yana fiskantar tambayoyi a ofishin jami’an shige da fice a filin jirgin. Amma za a miqa shi ga hukumar da ta kamata bayan sun kammala bincikar tasa. 

Rahotanni sun bayyana cewa, da ma tun lokacin da mutumin ya taso daga Houston ta Amurka, Kwanturolan filin jirgin Murtala Muhammad, CIS Kemi Nandap ya samu bayanan sirri a game da shi da muggan makaman da yake ɗauke da su, sakaye a cikin kayansa. 

Bayan shigowarsa Nijeriya ne kuma jami’an shige da gice suka cafke shi, tare da bincikarsa. Suka gano waɗannan makamai. 

Kodayake, an gano cewa yana ɗauke da wasu takardu na shaidar gwamnatin Amurka ta yarje masa amfani da bindigogi, duk da dai ba a tabbatar da sahihancinsu ba. Sai dai abin mamakin shi ne, yadda wannan Ba’amurke ya ƙi ya bayyana cewa yana ɗauke da waɗannan makamai ga jami’an tsaro yayin da ya shigo filin jirgin.