‘Yan sama jannatin dake cikin kumbon Shenzhou-13 sun sauka lami lafiya

Daga CMG HAUSA

‘Yan sama jannati 3 na ƙasar Sin, waɗanda su ne tawaga ta biyu da aka tura domin ginin tashar sararin samaniya ta ƙasar, sun kammala aikinsu na tsawon watanni 6, inda suka dawo doron duniya da safiyar yau Asabar 16 ga wata.

Dukkan ‘yan sama jannatin sun fito daga cikin ɓangaren dawowa na kumbon Shenzhou-13 cikin ƙoshin lafiya.

A ranar 16 ga watan Oktoban shekarar 2021 ne, aka harba kumbon na Shenzhou-13 daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan, inda ta hade da babban ɓangaren tashar sararin samaniya ta Tianhe. ‘Yan sama jannatin sun zauna cikin tashar ta sararin samaniya na tsawon watanni 6, inda suka kafa wani sabon tarihi na zaman ‘yan sama jannatin ƙasar Sin a sararin samaniya.

Nasarar kammala aikin kumbon Shenzhou-13 na ƙasar Sin, wata alama ce ta kammaluwar wani mataki na tantance wata muhimmiyar fasaha ta tashar ta sararin samaniya cikin nasarar, haka kuma tashar za ta shiga matakin gini.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *