Buhari zai ƙaddamar da aikin haƙo mai a Arewacin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

A ranar Talata ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo mai a Arewa wanda zai gudana a jihohin Bauchi da Gombe.

Aikin wanda zai gudana a yankin Kolmani shi ne irinsa na farko da Arewacin Nijerya ya taɓa gani.

Kimanin shekaru biyu da suka gabata aka gano arzikin man da ke kwance a yankin.

Duk da dai irin wannan aiki ba shi ne farau ba a Kudancin ƙasar, amma wannan shi zai zama karon farko Arewa bayan da matsalar tsaro ta hana aiwatar da makamacin aikin a yankin Borno.

Tun a 2016 Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), ya ƙaddamar da binciken gano mai a wasu jihohin Arewa, inda ya gano arzikin man a jihohi da suka haɗa da Bauchi, Gombe, Borno da kuma Neja.