Gwamnatin Tarayya ta fara karɓe kadarorin waɗanda ke ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A cigaba da daƙile ayyukan ta’addanci da ake fuskanta a lungu da saƙon ƙasar nan, Gwamnatin Nijeriya ta fara ƙoƙarin karɓe kadarorin waɗanda aka gano suna taimaka wa ko ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da kuɗaɗensu da shawarwarin su da dai sauransu don haɓaka ta’addanci a cikin ƙasar.

Kamar yadda wasu gidajen jaridu suka rawaito, sun ce jami’an tsaro da sauran hukumomin ƙwararru a kan lamuran tsaro suna bibiyar kadarorin masu taimaka wa ‘yan ta’adda da suka haɗa da kamfanoni da asusun ajiya na banki da kuma wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da ta’addanci a Nijeriya.

Rahoton ya bayyana cewa mutane 18, ƙungiyo da kuma kamfanoni suna cikin sunayen manyan masu laifuka da karya dokar ƙasa a ƙarƙashin kulawar kwamitin Manyan Masu Laifuka a Nijeriya, wato kwamitin da ya tattara dukkan ɓangarorin tsaro a ƙarƙashin sabuwar dokar ƙasa ta (Kiyayewa da kuma Hanawa) ta 2022.

Ƙungiyoyin sun haɗa da: Ƙungiyar da ke fafitukar kafa ƙasar Biyafara IPOB, Boko Haram, ISWAP, Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan, sai ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da kuma mutane 13 da aka samu da hannu wajen taimaka wa maharan Boko Haram da kuɗaɗe.

An gano cewa ƙungiyar IPOB tana samun kuɗaɗe ne daga wasu da suke taimaka wa ƙungiyar daga zama a ƙasashen waje da kuma masu ɗaukar nauyin watsa aikace-aikacen ƙungiyar a kafofin yanar gizo.

Sai kuma wasu da ke bada gudunmuwa ta hanyar karɓar kuɗin fansa daga yin garkuwa da mutane, satar shanu, fashi da makami da kuma tirsasa wa mutanen ƙauyaku biyan haraji da ƙarfi da yaji.

Kwamitin dai mai mutane 16, Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Nijeriya, Abubakar Malami SAN, ne ke jagorantar shi.

Sauran mambobin sun haɗa da: Ministar Kuɗi, Ministan Kula da Harkokin Kasashen Waje, sai kuma mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro a Nijeriya, Darakta-Janar na Hukumar DSS, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Sufeto-Janar sai Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya EFCC.

Kazalika a cikin mambobin kwamitin akwai: Shugaban Hukumar Hana Ci da Karɓar Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa ICPC, Shugaban Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi na Ƙasa NDLEA, Hukumar Tattara Haraji ta Tarayya, Darakta-Janar NIA, Wakilin CoDs, Darakta-Janar na Hukumar Daƙile Safarar Mutane Da Sauran Laifuka NAPTIP, Darakta na NUFIN a matsayin sakataren kwamitin; da kuma wasu mutane masumuhimmanci da Shugaban Ƙasa ya aminta da su a cikin kwamitin.

A cikin aikace-aikacensu, kwamitin yana da ikon samar da duk wasu tsare-tsare da sharuɗɗa a ƙarƙashin doka ta Sashe na 49, 53 da kuma ta 54 ta dokokin ta’addanci (Kiyayewa da Hanawa) ta 2022 da kuma bada shawara kan hanyar da za a wanzar da dokar bisa tsarin Jami’an tsaron Majalisar Dinkin Duniya wajen shawo kan matsalolin da suka shafi masu taimaka wa ta’addanci da zuba kuɗaɗensu a ciki da kuma danganta Ƙungiyar Haɗin kan Ƙasashen Afrika da kuma Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS).

Haka kuma, an umarci Ministan Shari’a na Nijeriya da ya daƙile waɗanda ake tuhumi da yin tafiye-tafiye, kulle asusan kuɗaɗensu, karɓe kadarori da kuma wasu abubuwa da suka shafi tattalin arzikin mutanen da ake zargi a cikin sunayen da ƙasar Turai ta ba Nijeriya.

Gwamnatin Nijeriya ta gano wasu masu ɗaukar nauyin ta’addanci 96, daga ciki akwai mutane 424 masu alaƙa ko taimakawa da kuɗaɗe wa ‘yan ta’adda, waɗanda aka karɓe kadarorinsu bayan bin hanyoyin da doka ta tanada

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana a watan Fabrairu, 2022 cewa jami’an tsaron farin kaya sun gano wasu kamfanoni 133 da cibiyoyin masu canjin kuɗaɗe guda 33 da ke da alaqa da ta’addanci a Nijeriya.

Akwai kuma wani rahoto da ke bayyana cewa ana cigaba da gudanar da gangamin ƙwamushe duk kadarorin ‘yan ta’adda da masu ɗaukar nauyinsu.

Da yake ƙarin haske a kan irin cigaban da ake samu ranar Alhamis ɗin da ta gabata, wani babban jami’i a Ma’aikatar Shari’a ya ce: “A zaman da kwamitin mu ya yi satin da ya gabata, mun gano tulin kadarori mallakin ‘yan ta’adda da kuma masu ɗaukar nauyinsu, amma ba mu fara karɓewa ba, muna aiki ne a kan hakan, muna jiran umarnin kotu don ta ba mu damar karɓewa da garƙame kadarorin.

“Kuma yanzu haka muna sa ido da binciken kamfanonin da ke da alaƙa ko ɗaukar nauyin ta’addanci; da zarar mun gudanar da bincike mun gano to za mu gabatar da qorafinmu a gaban kotu, amma dai ba mu zo nan ba tukunna.

“Haka kuma, mun gano wasu kadarori guda 6 na ƙungiyoyi ko cibiyoyi, inda muke cigaba da bincike don gano wasu kadarorin da kamfanoni na waɗannan mutane.

“Dukkanin asusun ajiyar kuɗaɗensu na banki mun garƙame su, amma dai ba mu binciko kadarorinsu na zahiri ba. Waɗanda muke da bayani a kan su, sune muke aiki a kai, jami’an mu da ke gudanar da bincike su ne suke ƙoƙarin binciko dukkan kadarorin da suka mallaka.”

Haka kuma, an gano mutane 13 a cikin sunayen, waɗanda ke ɗaukar nauyin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.

Sunayen waɗanda aka ƙara a cikin sabon daftarin sunayen su ne: Abdurrahaman Ado, Bashir Yusuf, Ibrahim Alhassan, Muhammad Isah, Salihu Adamu, Surajo Mohammad, Fannami Bukar, Muhammed Musa, Sahabi Ismail, Mohammed Buba, Alin Yar Yaya General Enterprises, K. Are Nigeria Limited da kuma Suhailah Bashir General Enterprises.
Shidan farko na masu ɗaukar nauyin Boko Haram da kuma kamfanoni uku an fara zarginsu ne tun a 2020 inda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abu Dhabi ta tuhimi kamfanin da tura wasu kuɗaɗe har Dala 782,000 daga Daular Larabawa UAE zuwa ga ‘yan ta’adda.

Wani kwamitin haɗin gwiwa da ya gudanar da bincike kan masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’addan, ya gano wani da ake tuhuma da taimaka wa ‘yan ta’adda da kuma ta’addanci. Wanda ake tuhumar da ke hulɗar haƙar gwal a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, da aka ce ya aike da Naira miliyan 560.

Kamfanin Alin Yar Yaya General Enterprises yana da alaƙa da Yusuf, wanda aka rufe a kurkuku shekaru 10 a Abu Dhabi.

Kamfanin mai adireshi No. 2 Danladi Auyo House, Wapa Ƙaramar Hukumar Fagge, Jihar Kano da aka yi wa rajista 15 ga Afrilu, 2016.

Are Nigeria Limited, an yi masa rajista 19 ga Satumba, 2019 na Surajo Muhammad, wanda aka yi wa ɗaurin rai da rai a Abu Dhabi akan taimaka wa ƙungiyar Boko Haram daga Dubai.

Suhailah Bashir General Enterprises, an yi mishi rajista 28 ga Nuwamba 2016, wanda ke da alaƙa da Yusuf, wanda ke tsare shekaru 10 a kurkukun UAE a kan haɗa kai da Boko Haram.

Haka kuma Yaya da Bashir Enterprises su ma an samu sunayensu a cikin daftarin masu ɗaukar nauyin ta’addancin ranar 8 ga Nuwamba, 2022.

A ranar 5 ga Yuli, 2022, kwamitin ya samu ƙarin wasu ƙungiyoyi kamar haka: Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati Wal-Jihad (Boko Haram), Islamic State West Africa Province, Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan, Ƙungiyar IPOB, ‘Yan bindiga da kuma ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane.

‘Yan bindiga da kuma ‘yan ta’adda, suna daga cikin ƙungiyar maharan da Gwamnatin Tarayya ta bayyana a matsayin ‘yan ta’adda 25 ga Nuwamba, 2021.

Ƙungiyon sun fara ƙaddamar da hare-harensu ne shekaru da yawa a jihohin Zamfara, Katsina, Kebbi, Kaduna, Sakkwato, idan suke iƙirarin qulla alaƙa da Ƙungiyar IS, Boko Haram, Jama’at Nasr al-Islam wal Muslimin da Al-Qaeda ta hanyar ƙaddamar da munanan hare-hare da nufin qara samun ta’addanci da kuma kuɗin taimaka wa ‘yan ta’addan a yankunan su.

A 2021, maharan sun kai hare-haren 2,883, inda hare-hare 51 aka ƙaddamar da shi kan bataliyar jami’an tsaro, sauran kuma a kan ƙauyaku da mutanen gari.