Aisha Buhari ta karye, an garzaya da ita asibiti

Daga WAKILINMU

An garzaya da Matar Shugaban Ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, zuwa asibitin Abuja sakamakon karyewa da ta yi a ƙarshen mako.

Duk da dai babu wani cikakken bayani dangane da yadda Aisha ta samu karayar, sai dai majiyarmu ta ce, “faɗuwa ta yi inda ta karye a ƙafa.”

Kafin faruwar lamarin, an shirya Aisha za ta shirya liyafar aure na bikin Bilkisu Rimi, ‘ya ga Jakadan Nijeriya a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Mohammed Rimi, ranar Lahadi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Idan za a iya tunawa, a ranar Alhamis da ta gabata Aisha Buhari ta ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC a Jihar Kwara.

Inda ta ce tana da wasu tsare-tsare masu muhimmanci da ta shirya wa mata son inganta rayuwarsu.