Daga CMG HAUSA
A yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron tattaunawar sabuwar hulɗar ƙasa da ƙasa kan nazarin sararin samaniya da aikin ƙirƙire-ƙirƙire tsakanin MƊD da Sin.
A cikin saƙonsa, Xi ya yi nuna cewa, a shekarun baya-baya nan, Sin ta himmantu wajen gudanar da ayyukan nazarin sararin samaniya, waɗanda suka taimaka wajen haɓaka ilmin Bil Adama kan sararin samaniya, da ƙara kawo alheri ga ɗaukacin Bil Adama baki ɗaya.
Aikin binciken sararin samaniya ba ya karewa.
Ƙasar Sin na fatan ƙara haɗa kai da ƙasa da ƙasa da haɓaka mu’ammala da haɗin gwiwa, da yin nazari kan sirrikan sararin samaniya tare, da amfani da sararin samaniya cikin lumana, da ingiza bunƙasuwar kimiyya da fasahar da za ta amfani al’ummar duniya.
An buɗe wannan taro ne a birnin Haikou na lardin Hainan.
Mai fassara: Amina Xu
