Zuwa ga gwamnati kan satar ɗanyen mai

Assalamu alaikum. Wannan wasiƙa za ta tafi ne zuwa ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.

Rukunin haramtattun bututan man fetur da jami’an tsaron Nijeriya ke ganowa na ƙara fito da matsalar satar man fili a ƙasar – wani abin al’ajabi hatta a yankin Neja-Delta da aka saba satar man.

A Jihar Delta, ɓarayi sun gina bututu mai tsawon kilomita 4 har zuwa Tekun Atalantika mai tsananin tsaro.

A can ne manyan jiragen ruwa masu tsawon ƙafa 24 ke yin lodin mai a filin Allah.

“Aiki ne na ƙwararru,” a cewar shugaban kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, Mele Kyari, yayin da yake zagayawa don ganin ɓarnar ɓarayin ke yi wa Nijeriya kai-tsaye a kafar talabijin.

Nijeriya ta dogara ne kacokam kan ɗanyen mai da take haƙowa kuma kuɗaɗen shigarta na cikin matsala saboda satar man, kamar yadda jami’ai ke faɗa.

Man da ƙasar ke haƙowa ya ragu daga ganga miliyan 2.5 a kowace rana a 2011 zuwa miliyan ɗaya da kaɗan a watan Yulin 2022, inji NNPC.

Hukumomi na cewa an yi asarar fiye da dala biliyan 3.3 sakamakon satar mai a shekarar da ta gabata a daidai lokacin da sauran ƙasashe masu arzikin mai ke samun maƙudan kuzi, ita kuwa Nijeriya ba ta iya cimma adadin da aka ƙayyade ma ta ba.

Kuma hakan ba ya nufin ba wata matsala ba ce idan ta yi asarar kuɗi saboda ɓarayin, akwai ɗimbin talauci a taksanin ‘yan ƙasa mai yawan gaske.

Akwai matsalolin cin hanci da rashawa, daga maganar tallafin mai – inda babu wanda yake tabbas na man da ake shiga da shi – zuwa samun lasisin mallakar rijiyar mai.

A 2019 ma, Wike ya zargi wani babban kwamandan soja da ƙarfafa wa ɓarayin fetur gwiwa, duk da cewa an musanta zargin.

Ganin cewa duka wannan na faruwa ne a ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne shugaban ƙasa kuma ministan mai, lamarin ya raunata yunƙurinsa na yaƙi da cin hanci da rashawa, a cewar Salaudeen Hashim na gidauniyar CLEEN Foundation mai yaƙi da rashawa.

“Ba lallai a gane cikakkiyar ɓarnar ba har sai gwanatinsa ta sauka daga mulki a watan Mayu,” kamar yadda wani mai sharhi ya faɗa wa manema labarai.

Jirgin ruwan da aka ƙona a kwanan nan bisa zargi dakon ɗanyen mai na sata mai yawan lita 650,000 a Delta ya jawo cecekuce.

Mutane da dama na tambayar me ya sa jami’an tsaro suka yi gaggawar ƙona hujjar – ɗaya daga cikin nasarorin da Tompolo ya yi a baya-bayan nan – amma hafsan tsaro na Nijeriya ya ce babu buƙatar bincike.

Yunƙurin Tompolo na taimakawa wajen daƙile satar man ta bai wa mutane mamaki. Yayin da ake biyan sa saboda aikin, ya bayyana irin ƙaunar da yake yi wa Nijeriya da kuma muhallin Neja-Delta, amma kuma shi ne mutumin da yake da tarihin fasa bututai masu yawa a baya.

Kamar yadda wani ƙwararre ya bayyana, bututan sata da ake ganowa a yanzu suna Delta ne, inda yake da ƙarfin iko sosai.

Abu ne mai wuya wani mutum ya yi amfani da su wajen ɗanyen mai tsawon shekaru a wannan yankin ba tare da saninsa ba, a cewarsu.

A baya, an sha fafatawa tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga amma yanzu abubuwa sun ɗan lafa a kwanakin nan, amma wasu na cewa yarjejeniya ce a tsakaninsu cewa kowa ya yi ‘harkasa’.

Waɗanda kawai abin zai dama su ne ’yan Nijeriya na gari, masu bin doka, da kuma ƙila kamfanonin man, waɗanda ba lallai a ji wani tausayinsu ba a faɗin ƙasar.

Muhammed Albarno, 08034400338.