Bunƙasa Ƙasa: Shugaban tsaro ya nemi a riƙa aikin jarida don raya ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya jaddada ƙoƙarin da sojojin Nijeriya suke yi na kare martabar ƙasar ta hanyar aikin jarida don raya ƙasa ta fuskar tattali da siyasa da sauran ababen more rayuwa.

Ya faɗi haka ne a yayin ganawa da wakilan labaran Tsaro da Kodinetan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci (NCTC) a birnin tarayya Abuja, ya na mai nuna muhimmancin wayar da kan al’umma da tabbatar da adalci acikin masu riƙe da madafun iko daga ƴan jaridu.

Ya ce aikin jarida don raya ƙasa zai bada damar ƙarfafa haɗin-gwiwa da ƴan jarida da gidajen jaridu wanda hakan zai taimaka wa haɗin-kai da ci-gaba acikin al’umma.

A nasa jawabin, Ministan Labarai da Wayar kan al’umma, Mohammed Idris, wanda Darakta-Janar na ‘Voice of Nigeria’ (VON), Jibril Baba Ndace ya wakilce shi, ya ce ƙoƙarin jami’an soji na faɗa da ta’addanci abu ne na a yaba, ba a kushe ba, ya na mai kira ga ƴan jarida da su girmama hakan.

Ya kuma yi kira ga gidajen jaridu su cigaba da bai wa Shugaba Bola Tinubu da sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya a ƙoƙarin su na samar da gobe mai kyau ga al’umma da ƙasar baki ɗaya.

By Babaji