Albashi: Tsofaffin sojojin Nijeriya sun garƙame Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu daga cikin sojojin Nijeriya da suka yi ritaya, a ƙarƙashin inuwar gamayyar ’yan fansho na soja a Abuja, sun garƙame ƙofar Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya a safiyar jiya Alhamis, saboda rashin biyan su ƙarin albashi daga kashi 20 zuwa 28 tun daga watan Janairu zuwa Nuwambar 2024.

Tsofaffin sojojin daga sassa daban-daban sun koka da yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza biyan su haƙƙoƙinsu.

Bukatun su sun haɗa da biyan kuɗaɗen tallafi daga Oktoba 2023 zuwa Nuwamba 2024, biyan Naira 32,000 da aka ƙara a fansho, biyan kuɗaɗen alawus na SDA a dunƙule da kuma dawo da kuɗaɗen da aka cire daga kuɗaɗen fansho na sojojin da dai sauransu.

A watan Disambar 2023, Majalisar Dattawa ta bayyana shirin fara cikakken bincike a kan Hukumar Fansho ta Soja bayan ta dawo daga hutu.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da kasafin kuɗi, Olamilekan Adeola ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kare rahotan kasafin kuɗin da kwamitin majalisar dattijai kan yi wa gwamnati hidima.

A zaman, an buƙaci ƙarin kuɗi da ya kai Naira biliyan 20, domin gina ofishin hukumar fansho ta sojoji, da kuma gyara kashi na 1 zuwa na 4 na sakatariyar gwamnatin tarayya.

Shugaban ya caccaki ayyukan hukumar da kasafin kuɗinta da kuma adadin waɗanda suka yi ritaya da aka ce ba sa karɓar albashi.

By ukarofi