Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) ta yi ƙiyasin cewa, bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya ya ragu zuwa mataki na kashi 3% a shekarar 2025 a cewar rahoton hukumar na baya-bayan nan game da hasashen tattalin arzikin duniya da aka fitar ranar Talata.
A sabon hasashen da ta fitar, hukumar ta ce tattalin arzikin duniya zai ƙaru da kashi 2.8 cikin ɗari a wannan shekarar, maimakon kashi 3.3 cikin ɗarin da ta yi hasashe a baya.
Amurka ta kasance ƙasar da hasashen ya ragu matuƙa, a cikin manyan ƙasashen da ke da bunƙasar tattalin arziki.
A yanzu ana tsammanin tattalin arzikinta zai ƙaru ne da kashi 1.8 cikin ɗari a wannan shekarar, maimakon ci gaban 2.7 cikin ɗarin da aka yi mata hasashen samu a baya.
IMF ta ce, tana ganin za a samu matsin tattalin arziki na kashi 40 cikin ɗari a Amurka, saboda yaƙin cacar baka na kasuwancin da ya biyo ƙarin harajin.
Hukumar ta kuma rage hasashen ci gaban da Birtaniya za ta samu a ɓangaren tattalin arziki a wannan shekarar zuwa kashi 1.1 cikin ɗari, a maimaikon kashi 1.6 cikin ɗari.
A cewar rahoton: “Ga yankin kudu da hamadar sahara, ana sa ran ci gaban zai ragu kaɗan daga kashi 4.0 cikin dari a shekarar 2024 zuwa kashi 3.8 a shekarar 2025, kafin murmurewa cikin ƙanƙanin lokaci zuwa kashi 4.2 a shekarar 2026.
“Daga cikin manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, an sake duba hasashen ci gaban Nijeriya da kashi 0.2 na shekarar 2025 da kashi 0.3 na 2026, saboda rage farashin mai.”
