Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni ta Nijeriya (CAC) ta cire kamfanoni sama da 80,000 daga rajistarta, saboda gaza biyan kuɗaɗen shigar shekara-shekara na tsawon shekaru 10.
Wannan matakin ya biyo bayan wa’adin watanni uku da aka bayar a watan Yulin 2024, inda aka shawarci kamfanonin da abin ya shafa su sabunta bayanansu don guje wa soke rajistarsu.
Hukumar CAC ta ce, ta yi waje da kamfanonin da suka kasa sabunta rahotonsu na shekara.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “jama’a za su iya tuna cewa hukumar ta fitar da sanarwar janye sunayen kamfanonin da hukumar ke da hujjar cewa ba sa gudanar da harkokin kasuwancin su yadda ya kamata saboda rashin shigar da kuɗaɗen shekara na tsawon wani lokaci na shekaru 10.
“An ba wa irin waɗannan kamfanoni wa’adin kwanaki 90 na doka don gabatar da abin da ake buƙata na dawowar shekara-shekara da aika [email protected]ɓ.ng. an cire imel zuwa kamfanonin da suka bi shawarwarin daga jerin.
“Hukumar bisa ga ikonta da aka bayar a sashe na 692 (4) na Dokar Kamfanoni da Allied Allied Matters Act No. 3 na 2020 ta soke sunayen kamfanonin da suka gaza ko kuma suka ƙi sabunta takardar dawowar shekara. An buga cikakken jeri akan gidan yanar gizon hukumar na www.cac.gov.ng.”
CAC ta ce, kamfanonin da aka cire daga rajistar ana ganin an rushe su daga ranar da aka buga su.
Hukumar ta ƙara da cewa, haramun ne a yi duk wani ciniki ko mu’amala da kamfanin da ya ruguje.
Wannan jarida ta bayar da rahoton cewa, kamfanoni 80,429 (biyar masu aiki, ɗaya ba tare da sabuntawa ba kuma 80,423 ba su aiki) ana tsammanin za a narkar da su saɓanin kamfanoni 100,000 da aka lissafa a baya.
Kamfanonin da aka cire sun haɗa da fitattun sunaye irin su Dunlop Nigeria Industries Sales Limited, Mitsubishi Shoji Kaisha Limited, Marina Inɓestment Limited da Jolly Food Industries.