Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) ta baiwa Nijeriya maki uku da ƙwallaye uku bayan rashin nasarar da aka samu kan wasan zagaye na huɗu na gasar cancantar shiga AFCON 2025 da aka shirya tsakanin Nijeriya da Libiya a ranar 15 ga Oktoba a Benina.
A hukuncin da ta yanke ranar Asabar, wanda shugaban hukumar, Ousmane Kane ya sanya wa hannu, hukumar ta yanke hukunci kamar haka:
1) An same hukumar ƙwallon ƙafa ta Libiya da karya dokar 31 na gasar cin kofin Afrika tare da dokoki na 82 da 151 na Kundin hukuncin CAF.
2) An ayyana wasan No. 87 Libiya da Nijeriya na cancantar shiga gasar cin Kofin Afrika na 2025 (wanda aka shirya yi a Benghazi ranar 15 ga Oktoba) a matsayin wanda Libiya ta rasa ta hanyar rashin halarta (da sakamakon 3-0).
3) An umarci hukumar ƙwallon ƙafa ta Libiya da ta biya tara ta dala 50,000.
4) Dole a biya tarar cikin kwana 60 daga lokacin da aka sanar da wannan hukuncin.
5) Duk wasu ƙorafe-ƙorafe da buƙatun neman babu su.
Hukuncin yana nufin cewa Nijeriya na kusa da samun tikitin shiga gasar AFCON 2025 da saura wasanni biyu. Super Eagles suna da maki 10 daga wasanni hudu, maki hudu sama da Benin da ke matsayi na biyu, yayin da Ruwanda ke da maki biyar.
Libiya, da ke matakin ƙarshe, tana da maki ɗaya kacal kuma ta fita daga cikin masu takarar shiga gasar.
Nasara ko kunnen doki da Cheetahs na Benin a Abidjan ranar Alhamis, 14 ga Nuwamba (wasa na zagaye na biyar) zai ba Super Eagles tikitin zuwa wasan AFCON a Morocco, Disamba 2025/Janairu 2026.