Irin rawar da Amurka ta taka wajen sakin shugaban Binance da ke tsare a Nijeriya

A ranar Alhamis, Amurka ta tura jirgi ɗauke da kayan jinya da jami’an sojoji guda shida domin ɗauko Tigran Gambaryan, babban jami’in kamfanin Binance Holdings Limited, daga Nijeriya.

A cewar jaridar The New York Times, Gambaryan ya bar Nijeriya bayan Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar safarar kuɗaɗe da ta shigar a kansa.

A baya, wannan jarida ta ruwaito cewa a ranar Laraba, Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar safarar kuɗaɗe da aka shigar a kan Gambaryan, wanda aka tsare, sakamakon matsalar lafiyarsa da kuma shiga tsakani ta diflomasiyya.

An tsare Gambaryan tun watan Fabrairu sakamakon ɗaukar matakin gwamnati kan kamfanin saboda zargin yaudara a kan darajar naira. Haka kuma, wani babban jami’in Binance na yanki, Nadeem Anjarwalla, an tsare shi tare da Gambaryan.

A watan Maris, Anjarwalla ya samu damar tserewa daga hannun ofishin mai ba da Shawara kan tsaron Ƙasa (ONSA), inda ya bar Gambaryan don fuskantar tuhume-tuhume shi kaɗai.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana cewa sakin Gambaryan ya nuna kyakkyawar alaƙa da haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu.

Sanarwar ta ce: “Amurka na godewa Gwamnatin Nijeriya saboda sakin ɗan Amurka Tigran Gambaryan bisa dalilan rashin lafiya, wanda ya bashi damar komawa Amurka don samun kulawar likita ta musamman da yake buƙata.

Ana sakin Mr. Gambaryan, na kira matarsa Yuki don sanar da ita wannan labari mai daɗi. Ina matuƙar godiya ga abokan aikinmu na Nijeriya da kuma haɗin kan da muka samu, wanda ya kai mu ga wannan matakin, kuma ina fatan ci gaba da aiki tare da su a ɓangarori da dama masu mahimmanci a dangantakar ƙasashenmu biyu.