Daga USMAN KAROFI
Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta tabbatar da kama da kuma ƙwace makami tare da tsare wani jami’in sojan ruwa, LS Akila A, wanda aka tura FOB Dansadua don Operation FANSAN YAMMA, bisa zargin buɗe wuta tare da kashe abokin aikinsa na soja a wani yanayi mai tattare da shakku.
Wannan ya fito ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan ayyukan watsa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya gabatar ga manema labarai a Abuja.
Sanarwar ta ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin. Janar Buba ya tabbatar da cewa bayan kammala binciken, za a kai shari’ar gaban kotun soji don yin hukunci kan irin waɗannan laifuka a tsakanin dakarun soja.
A cewar sanarwar, “Tsarin sanar da iyalan wanda ya rasu na ci gaba da gudana. Saboda haka, ba a fitar da sunansa ga jama’a ba tukuna. Duk da haka, za a bayyana sunan nan ba da jimawa ba.
Don haka, muna roƙon kafafen yaɗa labarai da su yi taka-tsantsan wajen ruwaito wannan labari domin kada su kara jefa iyalan mamacin cikin damuwa.