21
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yanzu haka dai waɗanda suka mallaki Babbar Difloma ta Ƙasa (HND) za a ɗauke su a matsayin malamai a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a ƙarƙashin sabbin tsare-tsaren aiki, kamar yadda Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa (NBTE), Farfesa Idris Mohammed Bugaje ya sanar. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Larabar da ta gabata yayin gabatar da sabbin tsare-tsaren aiki ga masu ruwa da tsaki a fannin kimiyyar ƙere-ƙere, kamar yadda shugabar ma’aikata, Dakta Folasade Yemi-Esan ta amince da shi. Ya ce a cikin sabbin tsare-tsare, an soke Malaman makarantar da…
