Labarai

‘Yan sanda sun bi umarnin kotu kan maido da motocin Matawalle da suka ƙwace

‘Yan sanda sun bi umarnin kotu kan maido da motocin Matawalle da suka ƙwace

Daga BASHIR ISAH Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta cika umarnin kotun da ya buƙaci ta maido da motocin da ta kwashe a gidajen tsohon Gwamnan Jihar, Bello Matawalle. A ranar 6 ga watan Yuni jami’an tsaro suka kai samame a gidajen Matawalle da ke Gusau da kuma yankin Ƙaramar Hukumar Maradun inda suka kwahe masa motoci kimanin guda 40 da sauran kadarorinsa. Jami’an tsaron dai sun ce, sun aikata hakan ne bisa umarnin da kotu ta ba su. Bayan ‘yan sa’o’i da kwashe motocin ne mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Suleiman Idris, ya fitar da sanarwar cewar jami’an…
Read More
Qausain TV Ta karrama Pantami da lambar yabo

Qausain TV Ta karrama Pantami da lambar yabo

An karrama tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da lambar yabo, mako biyu bayan kammala aiki a Gwamnatin Muhammadu Buhari. Fitacciyar Talabijin ta Qausain TV ce ta miƙa lambar yabon ga tsohon ministan a yayin ziyarar da shugabannin tashar suka kai masa a gidansa dake Abuja. A yayin bada lambar yabon, Shugaban Tashar, Nasir Musa Albani Agege ya bayyana Isa Ali Pantami a matsayin wata kadara ta Nijeriya, wanda ya ce sun yi la'akari da cancanta ne zalla sakamakon namijin ƙoƙarin da tsohon ministan ya nuna wajen inganta ɓangaren Sadarwa da Tattalin Arziki…
Read More
Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar bai wa ɗalibai rance

Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar bai wa ɗalibai rance

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe guda ɗaya inda ya sanya hannu a kan qudirin dokar bai wa ɗaliban Nijeriya lamuni kyauta domin biyan kuɗaɗen karatunsu. Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a ranar da Nijeriya ta ke bikin ranar dimokraɗiyya a ranar 12 ga watan Yuni. A cewar wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ne ya ɗauki nauyin gabatar da ƙudirin dokar inda majalisar ta zartar da shi. Dokar dai tana da takaitaccen takenta,…
Read More
Matasa na da rawar takawa wajen bunƙasa harkar kasuwanci a Kano – Abdul Aja

Matasa na da rawar takawa wajen bunƙasa harkar kasuwanci a Kano – Abdul Aja

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana cewa matasa suna da rawar da za su taka wajen cigaba da bunƙasa harkar kasuwanci a Jihar Kano. Alhaji Abdu Muhammad Aja, ɗaya daga cikin iyayen kasuwar Wapa ne ya bayyana hakan a lokacin da ake rantsarda sabbin zaɓaɓɓun ƙungiyar 'yan canji ta Al'amanat ta Wapa. Ya ce abin farin ciki shine sabon zaɓaɓɓen shugaban qungiyar Alhaji Sani Salisu Dada tun yana zagayen yaƙin zave ya ce yana neman taimakonsu a matsayinsu na iyayen ƙungiya da yayyen sa da sauran tsofaffin shugabanni. Ya fara da cewa in Allah ya so ya yarda zai…
Read More
Tinubu bai buɗe iyakokin Nijeriya ba – Kwastom

Tinubu bai buɗe iyakokin Nijeriya ba – Kwastom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Ƙasa (Kwastam) ta ce har yanzu Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bai sake buɗe dukkan iyakokin ƙasar nan da tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta rufe ba. Idan za a tuna a shekarar 2019 ne, Buhari ya rufe dukkan iyakokin ƙasar nan domin hana shigo da wasu kaya ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka haɗa da shinkafa, bindigogi da sauransu. Bayan shekaru biyu, gwamnatin Buhari ta sake buɗe wasu kaɗan daga cikin iyakokin, wasu kuma sun kasance a rufe duk da kokawar da ‘yan Nijeriya suka yi. A kwanakin baya…
Read More
Ƙungiyar Ƙabilar Gbagyi ta buƙaci Tinubu ya saka su cikin jerin ministocin sa

Ƙungiyar Ƙabilar Gbagyi ta buƙaci Tinubu ya saka su cikin jerin ministocin sa

Daga SANI AHMAD GIWA Ƙabilar Gbagyi, wadda ita ce mafi girma a yankin Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya saka su a cikin jerin sunayen ministocin da ke tafe. Misis Dorothy Nuhu Akenova, wata fitacciyar ‘yar ƙabilar Gbagyi ce ta yi wannan kiran a lokacin da take zantawa da manema labarai a Abuja, babban birnin Nijeriya ranar Juma’a, don roƙon a saka Gbagy a cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu. A cewarta Ƙungiyar Gbagyi ta buƙaci da kada a yi watsi da ƙabilarsu a lokacin da ake tsara jerin sunayen. Misis Akenova, wacce…
Read More
Gwamnan Zamfara ya nemi haɗin kan sojoji don yaƙi da matsalar tsaro

Gwamnan Zamfara ya nemi haɗin kan sojoji don yaƙi da matsalar tsaro

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, na ci gaba da neman haɗin kan rudunar sojoji domin magance matsalar tsaron da jiharsa ke fuskanta. A ranar Juma'a Gwamna Lawal ya ziyarci Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja inda suka yi tattaunawa ta musamman. Sanarwar da Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya rattaɓa wa hannu ta ce, ziyarar Lawal ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen yaƙi da matsalolin tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar. “Gwamna Lawal ya ziyarci Hedikwatar Tsaron ne musamman don…
Read More
Matan Nijeriya fiye da 25,000 sun maƙale a Mali – NAPTIP

Matan Nijeriya fiye da 25,000 sun maƙale a Mali – NAPTIP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar da ke Yaqi da Safarar Mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce aƙalla mata da ‘yan mata 'yan Nijeriya sama da 25,000 da aka yi safarar su ne suka maƙale a Mali. Kwamandan hukumar mai lura da shiyyar Benin, Mista Nduka Nwanwenne ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wani taron bita da aka shirya wa ƙwararru kan harkokin yaɗa labarai a birnin Legas. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ce an shirya taron bitar ne domin bunƙasa ƙwarewar mahalarta taron wajen wayar da kan jama’a kan illolin da ke tattare da…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka sace Hakimi da Dagaci a Jihar Bauchi

Yadda ‘yan bindiga suka sace Hakimi da Dagaci a Jihar Bauchi

Daga MU'AZU HARDAWA a Bauchi ‘Yan bindiga a ranar Asabar ɗin da ta gabata sun kashe wani babban ɗan kasuwa sannan sun yi garkuwa da wasu mutane uku da a cikinsu akwai dagacen garin Bakutunbe da hakimim Balma, Ƙaramar Hukumar Ningi. Shugaban Ƙaramar Hukumar Ningi Ibrahim Zubairu ya ce maharan sun yi garkuwa da hakimin Balma Hussain Saleh da dagacen Bakutunbe Idris Mai Unguwa sannan sun kashe wani babban ɗan kasuwa Haruna Dan-Oc. Wani mazaunin Balma da ba ya so a faɗi sunansa ya ce maharan sun tafi da hakimin da ƙarfe 11 na dare. ”Da suka shiga ƙauyen sai…
Read More
Kotu ta bai wa DSS sa’o’i 48 kan ta maido da kadarorin Matawalle da ta ƙwace

Kotu ta bai wa DSS sa’o’i 48 kan ta maido da kadarorin Matawalle da ta ƙwace

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ta bai wa sashen DSS na rundunar 'yan sandan jihar da sauran hukumomin tsaron da lamarin ya shafa umarnin su maido da motoci kimanin motoci 40 da sauran kadarorin tsohon Gwamnam Zamfara, Bello Matawalle, da suka ƙwace. Kotun ta ce, sa'o'i 48 kacal ta bai DSS don cika wannan umarni. Umarnin da kotun ta bayar a ranar Alhamis na zuwa ne biyo bayan samamen da jami'an DSS da na NSCDC suka kai gidajen tsohon Gwamna Matawalle a Gusau da Maradun a ranar 9 ga Yuni, inda…
Read More