Yadda ‘yan bindiga suka sace Hakimi da Dagaci a Jihar Bauchi

Daga MU’AZU HARDAWA a Bauchi

‘Yan bindiga a ranar Asabar ɗin da ta gabata sun kashe wani babban ɗan kasuwa sannan sun yi garkuwa da wasu mutane uku da a cikinsu akwai dagacen garin Bakutunbe da hakimim Balma, Ƙaramar Hukumar Ningi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ningi Ibrahim Zubairu ya ce maharan sun yi garkuwa da hakimin Balma Hussain Saleh da dagacen Bakutunbe Idris Mai Unguwa sannan sun kashe wani babban ɗan kasuwa Haruna Dan-Oc.

Wani mazaunin Balma da ba ya so a faɗi sunansa ya ce maharan sun tafi da hakimin da ƙarfe 11 na dare.

”Da suka shiga ƙauyen sai suka nufi gidan hakimin suna ta ɓarin wuta da bindigogin su. Daga nan ne mutane suka arce kowa ya yi ta kansa.

A wannan dare ‘yan bindigan sun afka ƙauyen Bakutunbe suka yi garkuwa da dagacen ƙauyen da wani Ya’u Gandu mai shekara 45.

Maharan na yi wa kowannen su kuɗi kan Naira miliyan 8 kuɗin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *