Labarai

Sarkin Musulmi ya bayyana ranar Babbar Sallah

Sarkin Musulmi ya bayyana ranar Babbar Sallah

Daga BASHIR ISAH Ranar 28 ga watan Yuni idan Allah Ya kai mu take Babbar Sallah (Idil Kabir) ta bana. Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III ne ya bayyana haka ranar Lahadi da daddare biyo bayan ganin jinjirin watan Zul-Hajja. Sarkin Musulmi ya ce sakamakon ganin jinjirin watan, ya tabbata yau (Litinin) 1 ga Zul-Hijja na shekarar 1444 wanda ya yi daidai da 19 ga Yunin 2023. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Shugaban Kwamitin Bada Shawara na Fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya…
Read More
Sanusi ya yi ganawar sirri da Tinubu

Sanusi ya yi ganawar sirri da Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A jiya Alhamis ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Sarkin Kano na 14 kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi (Khalifa Muhammadu Sanusi II), a fadar Aso Rock. Ziyarar ta Sanusi, wadda ita ce ta farko tun bayan da shugaban ƙasar ya hau karagar mulki, na zuwa ne mako guda bayan da shugaban ƙasar ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN. Ba a tantance tattaunawar da suka a wannan ganawa ta sirri ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto. Sanusi ya riƙe muƙamin shugaban CBN…
Read More
Tinubu ya amince da buƙatunmu har da N200,000 mafi ƙarancin albashi – TUC

Tinubu ya amince da buƙatunmu har da N200,000 mafi ƙarancin albashi – TUC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC, ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shirya yi, inda ta danganta matakin da Gwamnatin Tarayya qarqashin jagorancin Bola Tinubu ta cimma cika dukkan buƙatunsu. Da farko dai ƙungiyoyin awadagon sun ƙaddamar da yajin aikin ne sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi, wanda hakan ya haifar da ƙarin farashin man fetur da tsadar rayuwa. Babban maƙasudin yajin aikin dai shi ne matsawa Gwamnatin Tarayya lamba kan ta sauya ƙarin kashi 200 cikin 100 na farashin man fetur. Bayan tattaunawa da yawa da suka haɗa da wakilai daga gwamnatin…
Read More
Hajjin 2023: Yadda ake jigilar mahajjata cikin hanzari

Hajjin 2023: Yadda ake jigilar mahajjata cikin hanzari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Matsaloli da kurakuran da suka gabata kamar wuƙa ne, ko dai ta yi mana amfani ko kuma ta yanke mu, kuma ya dogara ne da yadda muka riqeta ta hanyar wajen kaifin ko kuma ta hannun riƙewa. Ana ci gaba da jigilar Maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 cikin wasu ƙalubale nan da can. Saurin da hawan jirgin ke tafiya ya saɓa wa ƙarancin aiki da aka kawo na tsawon sa'o'i masu yawa, ta yin amfani da ƙaramin jirgin da wasu masu jigilar Alhazai da aka naɗa da…
Read More
Umarnin Kotu: Ba mu hana Emefiele ganin iyali da lauyoyinsa ba – DSS

Umarnin Kotu: Ba mu hana Emefiele ganin iyali da lauyoyinsa ba – DSS

Daga BASHIR ISAH Hukumar tsaro ta DSS ta ce, an bai wa tsohon Gwmnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, damar ganin iyalinsa d likitocinsa tun kafin umarnin kotu a kan haka. Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa DSS umarni kan ta ƙyale Emefiele ya gana da iyalai da kuma lauyoyinsa. Sai dai cikin sanarwar da ta fitar ranar Asabar ta bakin kakakinta, Peter Afunanya, DSS ta ce ta rigaya ta bai wa tsohon Gwamnan na CBN damar ganawa da lauyoyin nasa tun kafin kotu ta ba da umarni. Sanarwar ta ƙara da cewa, DSS na…
Read More
Iyalan Nnamdi Kanu sun kori lauyoyinsa

Iyalan Nnamdi Kanu sun kori lauyoyinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Iyalan Shugaban Ƙungiyar Masu Fafutukar Kafa Ƙasar Biyafara (IPOB) da ake tsare da shi, Mazi Nnamdi Kanu, sun kori manyan lauyoyinsa, Mike Ozekhome, SAN; da Ifeanyi Ejiofor. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aanin Kanu, Kanunta Kanu, ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa na Tiwita a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2023. Zargin ƙin amincewa da lauyoyin suka yi na barin likitocin Kanu na ƙashin kansa su same shi domin yi masa tiyatar gaggawa ne babban dalilan ɗaukar matakin. Sanarwar mai taken ‘Sanarwar sallama’ a wani vangare tana cewa “Mik Ozekhome,…
Read More
Majalisar Dokoki ta yi na’am da dukkan matakan Tinubu ke ɗauka kawo yanzu – Akpabio

Majalisar Dokoki ta yi na’am da dukkan matakan Tinubu ke ɗauka kawo yanzu – Akpabio

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Majalisar Dattawa, Mista Godswill Akpabio, ya bayyana bayyana cewa, Majalisar Dokokin Nijeriya ta gamsu da ayyuka da matakan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka. Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawarsa da shugaban ƙasar. Ya ce, majalisar za ta haɗa hannu da vangaren zartarwa na gwamnati domin inganta rayuwar ’yan Nijeriya. “Shugaban ƙasa ya riga ya fara ayyuka, kawai yana buƙatar goyon bayanmu ne don cigaban ayyukan a ƙasa. Don haka, majalisar da za ta dawo…
Read More
Ku nemi watan Zul-Hijja ranar Lahadi, kiran Sarkin Musulmi ga al’ummar Musulmi

Ku nemi watan Zul-Hijja ranar Lahadi, kiran Sarkin Musulmi ga al’ummar Musulmi

Daga BASHIR ISAH Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Zul-Hijja na 1444 daga wannan Lahadin. Abubakar, wanda shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci na Nijeriya (NSCIA), ya ba da umarnin hakan ne cikin wata sanarwar da Farfesa Sambo Junaidu ya sanya wa hannu. Zul-Hijja shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci inda al'ummar Musulmi, musamman waɗanda Allah Ya hore musu halin tafiya, kan tafi aikin Hajji a ƙasa mai tsarki. Kazalika, a cikin watan ne ɗaukacin Musulmin duniya kan gudanar da bikin Eid-el-Kabir, wato Babbar…
Read More
Ɗaliban Jaimi’ar Tarayya a Gusau sun yi zanga-zanga kan sace abokan karatunsu

Ɗaliban Jaimi’ar Tarayya a Gusau sun yi zanga-zanga kan sace abokan karatunsu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗaruruwan ɗaliban Jami'ar Tarayya Gusau da ke Jihar Zamfara sun tare hanyar Gusau zuwa Kaduna domin nuna rashin jin daɗinsu game da sace ɗaliban jami'ar su biyar. A daren Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace ɗaliban makarantar lamarin da ya harzuƙa ɗaliban da suka rufe hanyar, wanda hakan ya sa masu ababen hawa da dama suka maƙale na tsawon sa’o’i. Ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi na tarwatsa ɗaliban ya ci tura, inda da yawa daga cikinsu ke zaune a kan babbar hanyar, inda suka yi kira ga hukumomin da suka…
Read More
An naɗa Ibrahim Garba Shuaibu sabon Sakataren Yaɗa Labaran Mataimakin Gwamnan Kano

An naɗa Ibrahim Garba Shuaibu sabon Sakataren Yaɗa Labaran Mataimakin Gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin Sakataren Yaɗa Labaran Mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo. Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Juma'a. Shuaibu ya yi karatun digirinsa na farko a jami’ar Bayero Kano, inda ya karanci Laburari, inda kuma yanzu haka yake digiri na biyu a kan 'PR'. kuma shi ne wakilin. Kafin naɗin nasa, shi ne Shugaban ƙungiyar ƴan jaridu masu aikewa da rahotanni daga Jihar Kano. kuma…
Read More