Ku nemi watan Zul-Hijja ranar Lahadi, kiran Sarkin Musulmi ga al’ummar Musulmi

Daga BASHIR ISAH

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Zul-Hijja na 1444 daga wannan Lahadin.

Abubakar, wanda shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci na Nijeriya (NSCIA), ya ba da umarnin hakan ne cikin wata sanarwar da Farfesa Sambo Junaidu ya sanya wa hannu.

Zul-Hijja shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci inda al’ummar Musulmi, musamman waɗanda Allah Ya hore musu halin tafiya, kan tafi aikin Hajji a ƙasa mai tsarki.

Kazalika, a cikin watan ne ɗaukacin Musulmin duniya kan gudanar da bikin Eid-el-Kabir, wato Babbar Sallah.

Sanarwar ta ce, “Ana sanar da al’ummar Musulmi cewa, ranar Lahai, 18 ga Yuni da ta yi daidai da 29 ga Zul-Ƙada, ita ce ranar da za a nemi watan Zul-Hijja na shekarar 1444 AH.

“Don haka ana buƙatar Musulmi su fara neman jinjirin wata ranar Lahadi, sannan a miƙa rahoton ganin watan ga Dagaci mafi kusa don tura rahoton gaba har zuwa fadar Sarkin Musulmi.”

Sanarwar ta kuma yi addu’ar Allah Ya taimaki al’ummar Musulmi wajen sauke nauyin da Musulunci ya ɗora musu.