Cire tallafin mai: An ware tallafin Naira biliyan 702 ga ma’aikata

*Amfani da fetur ya ragu daga lita miliyan 67 zuwa 40 kullum
*Tinubu na neman tallafin majalisa don samar da motoci masu lantarki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) ta bayyana a jiya Alhamis cewa, tana duba yiwuwar ware Naira biliyan 702 na kuɗin rayuwa a matsayin tallafu ga ma’aikatan gwamnati a wani ɓangare na matakan daƙile raɗaɗin cire tallafin man fetur.

A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar a ƙarshen taron na NEC wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya ce, shiga tsakani ya haɗa da ƙudirin da aka ba da shawarar daga Naira biliyan 23.5 zuwa Naira biliyan 45 a duk wata a matsayin alawus-alawus na man fetur ga ma’aikatan gwamnati.

“Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa NEC, ta samu shawarwari kan hanyoyi daban-daban da kuma yadda ƙasar nan za ta iya amfani da duk wani qarin da muke samu a cikin kuɗaɗen shiga don rage tasirin da hakan zai haifar ga rayuwar ma’aikatanmu.

“Don haka sai suka ba da shawarar a yi gyara, wanda aka ƙiyasta ya kai Naira biliyan 702.92 a matsayin wani ɓangare na alawus-alawus da ya kamata a ba su a matsayin na cire tallafin man fetur ga duk ma’aikata da kuma bayar da Naira biliyan 23 ko 25 duk wata don daqile raɗaɗin cire tallafin.

“Bugu da ƙari kan tallafin rage raɗaɗin, gwamnati ta duba dukkan batutuwa, ƙalubale da matsalolin gaba ɗaya sannan ta kafa wani ƙaramin kwamiti na majalisar da zai duba tare da fitar da wa’adin aiki domin tsara wuraren musamman inda wannan maganin zai iya fitowa da kuma yadda zai kasance, za a raba domin rage matsalar ma’aikata da sauran ƙungiyoyi masu rauni.

“Mambobin kwamitin sun haɗa da Gwamnan Jihar Kebbi a matsayin Shugaba; Anambra mai wakiltar shiyyar Kudu maso Gabas; Gwamnan Benue, Arewa ta Tsakiya; Gwamnan Kaduna, Arewa maso Yamma; Gwamnan Kuros Riba, Kudu maso Kudu; Oyo, Kudu maso Yamma; da Gwamnan Jihar Bauchi mai wakiltar Arewa maso Gabas
“Sauran hukumomin da abin ya shafa a cikin kwamitin sun haɗa da Ofishin Kasafin Kuɗi, wakilan Babban Bankin Nijeriya CBN, Ofishin Babban Lauyan Tarayya, Kamfanin Mai na Ƙasa NNPCL, Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Nijeriya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC da Rukayat El- Rufai.

“Za mu zauna nan da makonni biyu domin gabatar da shawarwari ga Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa domin yanke hukunci mai tsauri da za a ɗauka nan take don magance matsalar da ake fuskanta ta hanyar cire tallafin,” inji shi.

Shi ma da yake nasa jawabin, Gwamna Umar Radda na jihar Katsina majalisar ta kuma tattauna kan matakan rage raɗaɗin domin daƙile illolin cire tallafin ta hanyar shirin NG-Cares.

“Kamar yadda kuka sani, Shirin NG-Cares shiri ne wanda ya fara 2021 yana gudana har zuwa 2024. Sannan kuma shine samar da wasu abubuwan gaggawa kan abubuwan jin daɗi, buƙatun jama’a kan batutuwa da dama tun daga ƙananan manoma, MSMEs da sauransu. Dala miliyan 750 ne daga asusun Bankin Duniya da suka taimaka kuma an fara da daɗewa,” inji shi.

Ya ce wasu daga cikin shawarwarin da aka bayar sun haɗa da cewa ya kamata jihohi su samar da hanyoyin da za su iya ɗaukar nauyin aiwatar da ayyukan jinƙai ga talakawa da marasa galihu, gidaje da manoma, gami da haɓaka tattalin arzikin ma’aikata na cikin gida.

“Za a iya samun ƙarin kuɗaɗe daga Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya, abokan cigaba da kuma kamfanoni masu zaman kansu na Nijeriya.

“Musamman, ana iya tuntuvar Bankin Duniya don ƙarin tallafi kan shirin NG-Cares. Za a iya fara tattaunawa da wuri-wuri. To waɗannan sune shawarwarin da aka bayar. Kuma Majalisar Tattalin Arziki za ta bi waɗannan shawarwarin don amfanin ‘yan Nijeriya, marasa galihu da talakawa,” inji shi.

A nasa jawabin, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya ce masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da iskar gas sun bayyana wa majalisar yadda za a rage farashin man fetur.

Ya ce ƙwararrun masana’antar sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta rage harajin da ake biya na man fetur da NPA da NIMASA da sauran hukumomin gwamnati ke karɓa.

Babban Manajan Darakta na Kamfanin mai na Nijeriya NNPCL, Mista Mele Kyari ya ce farashin man fetur a ƙasashen da ke makwabtaka da shi ya yi tashin gwauron zabi bayan cire tallafin da aka yi.

Ya ce ƙasashen dake makwabtaka da Nijeriya sun dogara ne da tallafin man fetur daga Nijeriya.

Ya ce shugaban na NNPC ya bada shawarar cewa ya kamata Nijeriya ta riƙa fitar da man fetur zuwa makwabtan da ke da qarancin ƙarfin shigo da man.

“GCEO na NNPC ya ce matsayin NNPC a da ya kasance a cikin harkar kasuwanci na zahirin cinikin man fetur ga ƙasashen makwabta. Tun da ba su da abin da za su iya shigo da man fetur.

“Mun yanke shawarar cewa za mu samu wani ƙaramin kwamiti na Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa mai kula da mai da iskar gas wanda zai duba batutuwan da aka kawo a gaba ko kuma ‘yan kasuwa, da Kamfanin da ke Kula da Harkokin Man Fetur na Ƙasa NNPC, don tabbatar da cewa mun daidaita rahoton da za a mayar wa Majalisar ta NEC da kuma idan majalisar ta yi watsi da batun za mu karve shi mu gabatar da shi ga Shugaban Ƙasa,” inji shi.

Gwamnan ya ce farashin man fetur zai ragu da Naira 40 idan matatun man ƙasar suka fara aiki gadan-gadan.

Shi ma da yake nasa jawabin, Gwamna Alex Otti na jihar Abia, ya ce a wani jawabi da hukumar kula da kera motoci ta ƙasa ta gudanar ya nuna cewa, kimanin jihohi shida na ƙasar nan da suka haɗa da Legas, Ogun, Anambra, Enugu, Akwa Ibom, Kaduna da Kano tuni suka fara cin gajiyar fasahar cikin gida, ababen hawa ko harhaɗa motocin da kamfanonin Nijeriya ke yi masu amfani da wutar lantarki.

Ya lissafa kamfanonin da suka haɗa da INNOSON, Maikano, Ɗangote Peugeot, Peugeot Automobile of Nigeria, Stallion Hundai, Honda, Elizade/Toyota, Coscharis da Ford, Kojo Motors da Jet Systems Motors.

“A halin yanzu, kusan 50,000 ne aka samar da ayyukan yi ta hanyar wannan aiki mai sauƙi na haɗa motoci a Nijeriya ko kuma samar da su a Nijeriya, ya ƙara da cewa hakan na iya ƙaruwa zuwa miliyan ɗaya, tare da tallafin Gwamnatin Tarayya.

“Abin farin ciki ne cewa wasu daga cikin waɗannan kamfanoni sun shiga ƙera ko haxa motoci masu amfani da wutar lantarki da motocin da CNG – matsananciyar iskar gas. Tasirin hakan shi ne cewa za a rage matsin farashin man fetur musamman yawan amfani da motocin lantarki da motocin CNG masu amfani da wutar lantarki.

“Da farko, ta rage yawan amfani da ita daga kusan lita miliyan 66, 67 a rana zuwa kusan miliyan 40. Kuma yayin da lokaci ya ci gaba, za a cigaba da samun raguwa,” inji shi.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce majalisar ta kuma tattauna kan matsalar ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar nan.

Ya ce domin rage wahalhalun da bala’in ambaliyan ruwa ya rutsa da su a faɗin jihohin da abin ya shafa a tarayyar ya bada shawarar gwamnatin tarayya ta sa baki ta hanyar sakin kuɗaɗen da suka dace ba tare da ɓata lokaci ba.

“Hakan zai taimaka wajen magance buƙatun waɗanda abin ya shafa tare da biyan basussukan da wasu jihohi suka ciwo a yunƙurinsu na taimakawa waɗanda abin ya shafa,” inji shi.

Ya ce kuma, an umurci ‘yan majalisar da su tuntuɓi Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Kamfanoni Masu Zaman Kansu da sauran ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa domin su taimaka wajen magance ambaliyar ruwa a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *