Labarai

Tsohon Gwamnan Binuwai, Samuel Ottom ya amsa gayyatar EFCC

Tsohon Gwamnan Binuwai, Samuel Ottom ya amsa gayyatar EFCC

Tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya amsa gayyatar Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Ta'annati (EFCC). A ranar Talata EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan don amsa mata tambayoyi kan abin da ya shafi zamanin mulkinsa. Majiyarmu ta ce Ortom ya isa harabar ofishin hukumar da ke Makurdi ne da misalin ƙarfe 10:08 na safe. Ƙarin bayani na tafe...
Read More
Tinubu zai yi ziyarar aiki ta farko tun bayan kama mulki

Tinubu zai yi ziyarar aiki ta farko tun bayan kama mulki

Daga BASHIR ISAH Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tafi ziyarar aiki Paris, babban birnin ƙasar Faransa ya zuwa ranar Alhamis, 22 ga Yuni. Wannan ita ce ziyara ta farko da Tinubu zai yi a matsayin Shugaban Ƙasa. Tinubu zai yi ziyarar ce domin halartar taron shugabannin duniya inda za su rattaɓa hannu kan Sabuwar Dokar Kuɗi ta Duniya wadda za ta da ba da fifiko kan ƙasashe marasa ƙarfi wajen samun tallafi da zuba jari biyo bayan matsanancin sauyin yanayi da kuma bayan tasirin annobar Korona. Taron wanda na yini biyu ne, zai gudana ne daga ranar 22 zuwa 23…
Read More
Bill Gates da Ɗangote sun jinjina wa Tinubu kan cire tallafin

Bill Gates da Ɗangote sun jinjina wa Tinubu kan cire tallafin

Daga BASHIR ISAH Hamshaƙin ɗan kasuwar nan Aliko Ɗangote da takwaransa Bill Gates da ya kasance Shugaban Bill and Melinda Gates Foundation, sun taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cire tallafin man da ya yi haɗi da sauran nasarorin da ya samu ya zuwa yanzu. Ɗangote ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da manema labaran Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan ganawarsu da Shugaba Tinubu a ofishinsa a ranar Litinin. A cewar Ɗangote, ana sa ran cire tallafin ya zama mabuɗi na hanyoyin samun ƙarin kuɗaɗe ga ƙasa don bai wa gwamnati zarafin zuba jari a sauran…
Read More
Gwamnan Zamfara ya buƙaci a maida hanyar Funtua-Gusau ta zama tagwaye

Gwamnan Zamfara ya buƙaci a maida hanyar Funtua-Gusau ta zama tagwaye

Daga BASHIR ISAH Gwamna Duada Lawal na Jihar Zamfara, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da tagwayen hanyoyi a hanyar Gusau zuwa Funtua domin bunƙasa cigaban jihar. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Nuhu Salihu, ya fitar ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar. Gwamna Lawal ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki wa Babban Sakataren Ma'aikatar Ayyuka ta Tarayya, Mamuda Mamman, a ofishinsa. Ya ce hakan ɓangare ne na alƙauran da ya yi wa talakawansa a lokacin neman zaɓe. Ya ƙara da cewa, mayar da…
Read More
Shugaba Tinubu ya rushe hukumomin gudanarwa na ma’aikatun gwamnati

Shugaba Tinubu ya rushe hukumomin gudanarwa na ma’aikatun gwamnati

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da rushe duka hukumomin gudanarwa na ma'aikatu da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya haɗi da na kamfanoni mallakar gwamnatin. Tinubu ya yi hakan ne domin sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora masa don amfanin al'umma. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Darktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar. Sanarwar ta ce rushewar ta fara aiki ne nan take ba da ɓata lokaci ba. "Sai dai rushewar ba ta shafi hukumomi da cibiyoyin da ke lissafe cikin Zubi na Uku, Kashi na 1, Sashe…
Read More
Tinubu ya naɗa Nuhu Ribaɗu da wasu a shugabancin fannin tsaro

Tinubu ya naɗa Nuhu Ribaɗu da wasu a shugabancin fannin tsaro

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin Shugaban Ƙasa sauke duka jami'an da ke jan ragamar fannin tsaron Nijeriya nan take. Kazalika, ba tare da ɓata lokaci ba Tinubun ya amince da naɗin waɗanda za su maye gurbin saukakkun. Waɗanda sabbin naɗe-naɗen ya shafa sun haɗa da: 1 Malam Nuhu Ribadu, Mai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha'anin Tsaro2 Manjo Janar C.G Musa, Babban Hafsan Tsaro3 Manjo T. A Lagbaja, Babban Hafsan Sojoji4 Rear Admirral E. A Ogalla, Babban Hafsan Sojojin Ruwa5 AVM H.B Abubakar, Babban Hafsan Mayaƙan Sama6 DIG Kayode Egbetokun, Muƙaddashin Sufeto-Janar na 'Yan Sanda7 Manjo Janar EPA Undiandeye,…
Read More
Tinubu ya sauke shugabannin tsaro

Tinubu ya sauke shugabannin tsaro

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauke shugabannin tsaron Nijeriya baki ɗaya. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar a ranar Litinin. Tinubu ya bi bayan sauke jami'an da naɗa sabbin da za su maye gurbinsu. A cewar sanarwar, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da ritayar dukkan shugabannin tsaro da Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, masu ba da shawara da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam." Sanar ta ƙara da cewa, sauke su ɗin ya fara aiki ne nan take, haka ma waɗanda aka naɗa…
Read More
Nijeriya ta sake ƙwato kambunta na ƙasar da ta fi zarra a samar da man fetur a Afirka

Nijeriya ta sake ƙwato kambunta na ƙasar da ta fi zarra a samar da man fetur a Afirka

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai ƙasar Nijeriya ta sake yi wa ƙasar Angola fintinkau a matsayin ƙasa mai samar da mafi yawan man fetur a Afirka. Wato kenan ta sake ƙwato kambunta wanda aka santa da shi a baya a matsayin ƙasar da ta fi kowacce samar da man fetur a Afirka. Wannna bayani yana ƙunshe ne a wani jawabi da ƙungiyar ƙasashe masu samar da man fetur (OPEC) rmta saki game da samar da ɗanyen man fetur a cikin watan Mayun 2023. Amma a watan Afrilu ƙasar Angola ta kere Nijeriya wajen samar da man fetur…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe basarake da ‘ya’yansa huɗu a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe basarake da ‘ya’yansa huɗu a Kaduna

Daga WAKILINMU Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe Arɗon Birni da Kewaye na Masarautar Zazzau, wato Alhaji Shuaibu Mohammed tare kuma da wasu 'ya'yansa huɗu. Lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare a ƙauyen Dorayi da ke Ƙaramar Hukumar Zaria, Jihar Kaduna. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, 'yan bindigar kimanin su biyar, sun kuma yi awon gaba da shanu 100 mallakar basaraken. Matar marigayin, Malama Halima Shuaibu, ta faɗa wa manema labarai cewa maharan sun harbi magidan nata ne da bindiga a kai wanda hakan ya yi ajalinsa nan take. Matar ta ce, “An fito…
Read More
Layin lantarki na Shiroro-Kaduna ya lalace – KEDCO

Layin lantarki na Shiroro-Kaduna ya lalace – KEDCO

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO, ya yi ƙarin haske dangane da ƙarancin wutar lantarki da ake fuskanta a jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa. Kamfanin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi wadda shugaban sashen yaɗa labaran kamfanin, Sani Bala Sani, ya sanya ma hannu ta ce, lamarin ya faru ne sakamakon lalacewar layin wutar na Shiroro-Kaduna 330KV. Kamfanin ya bayyana cewa tuni dai TCN ta fara aikin gyaran layin wutar wanda ake saran kammalawa a jiya lahadi. Daga ƙarshe ya bai wa al'umma haƙuri tare da bada tabbacin…
Read More