Tinubu ya sauke shugabannin tsaro

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauke shugabannin tsaron Nijeriya baki ɗaya.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar a ranar Litinin.

Tinubu ya bi bayan sauke jami’an da naɗa sabbin da za su maye gurbinsu.

A cewar sanarwar, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da ritayar dukkan shugabannin tsaro da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, masu ba da shawara da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam.”

Sanar ta ƙara da cewa, sauke su ɗin ya fara aiki ne nan take, haka ma waɗanda aka naɗa don maye gurbinsu.

Willie Bassey ya ba da sanarwar ce a madadin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *