Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Ba wani babban dalili ne ya sa a ke ayyana masu rawa da bazar wasu ko waɗanda ba su da ra’ayin kan su a matsayin ’yan amshin shata ba sai don yadda marigayi Dokta Mamman Shata ke waƙarsa a na yi ma sa amshi ba ragi ko kari.
Akwai ma wata waƙar Shata da komai ya ce sai ’yan amshi su ce “HAKANAN NE MAMMAN SHATA IDI ƊAN YELWA.”
Duk da ba labarin Shata na ke son yi a nan ba amma haƙiƙa an shan shaharar Shata da baiwar da Allah ya yi ma sa ta daban ce don haka in ’yan amshin sa sun biye ma sa ba za a yi mamaki ba.
Idan za a samu masu amshin Shata su na yin amshin ga Shatan su mai basira da sanin abun da ya ke yi to zai yiwu amshin ya yi amfani ko ma a ci rabarsa. Illar ta kan faru ne lokacin da ’yan amshin ke aikin baban-giwa wajen amsawa wanda wa imma bai san abun da ya ke yi ba ko kuma son zuciya kawai ya ke yayatawa.
Yaya za a iya samun ingantacciyar gwamnatin dimokraɗiiyya a yanayin da sashe ɗaya ya mallake ikon fada a ji ko sai abun da ya ke so a ke yi? Kirarin da a ke yi wa mulkin dimokurxiyya shi ne gwamnatin jama’a, daga jama’a zuwa ga hidimar jama’a.
Kazalika tsarin jagaorancin ya na da rassa uku da kowane a ke so ya yi aiki ba tare da katsalandan na ɗaya ɓangaren ba. Sashen zartarwa, majalisa da sashen shrai’a.
Sau da dama a kan samu sashen zartarwa na mamaye ikon sauran sassan biyu inda kuma yin hakan sam ba alheri ba ne a ƙasa.
A lokacin da sashen zartarwa ya kawo ƙuduri gaban majalisa a na son ta zauna ta yi muhawara ta tantance don amincewa ko sake buƙatar sashen zartarawa ya duba don yin gyra a wasu sassa ko ma sauya ƙudurin gaba ɗaya don ya amfani jama’a.
Majalisa kai tsaye wakilan jama’a ne daga dukkan sassan qasa. Ta nan tsarin dimokurɗiyya ke son duk abun da a ka kawo da ya shafi rayuwar jama’a ‘yan majalisa su koma wajen jama’ar don tambayar su ra’ayoyin su da hakan zai ba da damar ɗaukar matakin da zai fi zama alheri.
Duk wannan tsari ba zai tafi yadda ya dace matuƙar shugabannin majalisa masu ikon buga guduma don ƙuduri ya tabbata sun zama masu kare muradun sashen zartarwa ne ko jam’iyyarsu maimakon na waɗanda su ke wakilta ko kuma don amfanin ƙasa baki ɗaya.
In za a tuna cikin ikon Allah a 2007 lokacin da tsohon shugaba Obasanjo ya so zarcewa bisa mulki karo nauku ya yi iya bakin ƙoƙarin sa wajen samun amincewar majalisar amma ba mamaki don rashin amincewar jama’ada kuma duba hakan ba alheri ba ne ga ƙasa majalisar ta ai amincewa.
Wataƙila wataran in an samu tsohon Shugaban Majalisar Dattawa a lokacin Ken Nnamani da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Aminu Bello Masari za su yi bayani yadda a ka kaucewa canja tsarin mulki da zai ba wa Obasanjo damar mulkin rai-da-rai.
Albarkacin wancan matakin ya ƙaddara a ka yi shugaba Umar Musa ‘Yar’adu, Goodluck Jonathan, Muhammadu Buhari ga shi yanzu an samu Bola Ahmed Tinubu. Duk wanda ya samu yin mulki na shekaru 4 sau biyu duk tasirin sa sai ya sauka a zava ko a ɗora wani.
Wannan shi ne irin tsarin da Nijeriya ta ɗauko daga Amurka. Ku tuna irin shugabannin Amurka da su ka yi suna Ronald Reagan, Bill Clinton, Barack Obama da sauran su duk wa’adi biyu su ka yin a shekaru 8 kuma ba wanda ya yi yunƙurin sai ya sauya tsarin mulki don ya yi ta mulki har ƙarshen rayauwarsa.
’Yan takarar gwamnati sun zama shugabannin Majalisar Dokokin Nijeriya;
‘Yan takarar gwamnatin Nijeriya na jam’iyyar APC sun zama shugabannin Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 biyo bayan zaɓen da ya gudana a majalisar.
Godswill Akpabio wanda ɗan takarar shugaba Tinubu ne kuma gwanin jam’iyyar APC ya zama Shugaban Majalisar Dattawa inda Barau Jibrin daga Kano ya zama mataimakin shugaban majalisar.
A majalisar wakilai ma ɗan takarar gwamnati Tajudeen Abbas ya zama kakaki inda Benjmain Kalu ya zama mataimaki.
Tsohon gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari ya ƙalubalanci Akpabio a takarar inda ya samu quri’un da ba a yi tsammani ba duk da ba shi da goyon bayan gwamnati.
Yayin da Akpabio ya samu ƙuri’u 63 Yari ya samu 43 cikin adadin ‘yan majalisar dattawan 109.
Tajudeen Abbas ya samu ɗimbin quri’u 353 a cikin ‘yan majalisar 360. Waɗanda su ka yi hamayya da shi tsohon mataimakin kakakin majalisar Ahmad Idris Wase da Sani Jaji daga Zamfara sun samu ƙuri’a uku-uku.
Shugaba Tinubu ya taya waɗanda su ka lashe zaɓen murna da jajantawa ko yabawa waɗanda su ka yi hamayya don yadda ya nuna sun sa zaɓen ya ƙayatar.
Tinubu ya ce zai yi alaƙa da majalisar don kare muradun kasa da hakan ya nuna ya na gujewa zargin kar a ce zai maida shugabannin majalisar ’yan amshin shatan sa. An ga hoton Tinubu da sabon shugaban majalisar Akpabio su na dariya.
Za a yi fatan dariyar ta murnar nasara ce don fara yi wa kasa aikin da ya dace ba haɗa baki don kare muradun gefe ɗaya ba.
Magoya bayan ‘yan majalisar dokokin Nijeriya ta 10 sun yi dafifi a Abuja don taya gwanayen su da a ka rantsar murna.
Bakin sun shigo Abuja daga kusan duk sassan Nijeriya don taya ‘yan majalisar da a ka rantsar murna da kuma wasun su sun yi amfani da damar wajen kara ƙarfafa alaƙar su da ‘yan majalisar.
A irin wannan lokaci ‘yan majalisar kan yi amfani da gidajen su da kuma kama masaukan baƙi a Abuja don saukar magoya bayan hakanan su kan ma shirya liyafa.
Wani abu da kan faru shi ne yin ihsani ga magoya bayan da biyan kuɗin shatar motoci da su kan ɗauka don yin tururuwa don ganarwa idon su komai.
Matan ‘yan majalisar ma ba a barin su a baya a wannan lokaci inda su kan so kutsawa don a dama da su ko a toya duk wainar a gaban su kamarorin gidajen talabijin na ɗaukar hotunan su.
Duk bayan liyafar nan mafi a’ala a samu ‘yan majalisar da dagewa wajen wakiltar kwarai ga wadanda su ka turo su ko kuma ko ma ta yaya su ka zo, su tabbatar sun yi wakilci nagartacce ga mazaɓun su.
Sanata Adamu Bulkwachuwa da ya wakilici mazavar majalisar dattawa daga Bauchi ta arewa ya fasa kwai cewa ya shiga cikin ayyukan matar sa a lokacin ta na matsayin shugabar kotun ɗaukaka kara.
Adamu Bulkachuwa wanda bai samu nasarar dawowa majalisa ta 10 ba; shi ne mijin mai shari’a Zainab Bulkachuwa wacce ta yi ritaya a matsayin shugabar kotun ɗaukaka qara bayan cikar ta shekaru 70 na yin ritayar alƙalai.
Ɗan majalisar ya ce, ya shiga ‘yancin Zainab inda ya sa ta taimakawa wasu daga cikin abokan aikinsa a majalisar.
Tsohon shugaban majalisar Ahmed Lawan a lokacin kalaman a liyafar bankwana ya yi ta ƙoƙarin katsalandan a bayanan na Bulkachuwa don hana shi fasa kwai a iya gaskiyar abubuwan da ya ke son ba da bayanan sun faru.
Hakika irin wannan kan zama ƙarfafa zargin sashen shari’ar Nijeriya na yin abubuwan da ba su kamata ba.
Gabanin zaɓen shugabannin, mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce, a shirye ya ke ya durƙusawa ‘yan majalisar dattawa don su zaɓi Godswill Akpabio ya zama sabon Shugaban Majalisar Dattawa.
Shettima na magana ne a ganawa da ‘yan majalisar dattawan kan shirin zaɓen shugabannin majalisar.
A nan Shettima ya furta cewa mafi lalacewar ɗan takara kirista daga kudu ya fi mafi cancantar Musulmi daga Arewa.
Shettima ya ƙara da cewa, a kasa da a ke da shugaban kasa musulmi, mataimaki Musulmi ya dace don adalci mai matsayi na uku wato Shugaban Majalisar Dattawa ya zama Kirista.
Kalaman na Shettima sun jawo suka mai zafi daga wasu musamman a arewa inda su ke cewa bai kyautata kalamai ba ko da kuwa matsayar ta sa ba ta da illa. Ma’ana masu caccakar Shettima na cewa ba sai ya yi wannan kwatancen don tunanin burge wani ko samun karvuwa ba; cikin sauƙi zai nuna don a samu karin hadin kan kasa a miƙa ragamar majalisar ga kirista kuma daga kudu shikenan.
A tsarin mulkin Nijeriya duk wanda ‘yan majalisa su ka zaɓa zai iya zama shugabansu kuma ko da duk shugabannin daga gida ɗaya su ka fito.
Kammalawa;
Yanzu za a zuba ido a ga yadda majalisar za ta yi kamun ludayi do yiwuwa ko akasin haka na samun bambanci daga majalisa ta 9 da a ka zarga da zama ’yar amshin shatan tsohuwar gwamnatin Buhari. Ba lalle sai an yi fito na fito tsakanin majalisa ne za a gane akwai canji ba, a’a a na son a ga a na muhawara da fidda bayanan filla-filla kafin amincewa ko ƙin amincewa.
Babban haƙƙi ya rataya ga sabbin shugabannin su zama masu adalci da hikima wajen jagoranci fiye da bin ra’ayin shugaba Tinubu ko jam’iyyar APC.