Labarai

Gwamnatin Kano ta fara bincike kan zaftare wa ma’aikata albashi

Gwamnatin Kano ta fara bincike kan zaftare wa ma’aikata albashi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da cire Naira 370 na kowane wata daga albashi da fansho na ma’aikatan gwamnatin jihar. Sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi a wata takarda da ya aike wa ɗaukacin shugabannin hukumomin a ranar Litinin wacce Manhaja ta gani a ranar Talata ta ce, an dakatar da cire kuɗaɗen nan take har sai an kammala bincike kan tsarin. Gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ce ta ƙaddamar da wannan tsarin wanda ake zuba kuɗaɗen da aka cire a asusun wani kamfani mai suna Share Benefit Investment Limited. Sakataren ya…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum uku a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe mutum uku a Kaduna

Sun yi garkuwa da wasu da dama Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga Jihar Kaduna sun ce, aƙalla mutum uku sun mutu yayin da aka yi garkuwa da wasu dama sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai garin Sabon Layi cikin yankin Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari da ke jihar. Duk da dai ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a hukumance kan batun daga ɓangaren hukuma, sai dai wani jigo a yankin da lamarin ya faru, Anas Musa, ya tabbatar da aukuwar harin ga jaridar News Point Nigeria a ranar Juma'a. A cewar Musa, 'yan bindigar sun dira ƙauyen ne da…
Read More
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata batun yi wa Tinubu da gwamnoni ƙarin albashi

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata batun yi wa Tinubu da gwamnoni ƙarin albashi

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bai amince da wani ƙarin albashi ga zaɓaɓɓun 'yan siyasa da ma'aikatan fannin shari'a ba kamar yadda rahotanni suka nuna. Mai magana da yawun Tinubu, Dele Alake, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis. Alake ya bayyana haka ne a matsayin martani ga rahoton da aka yaɗa kan cewa Shugaban Ƙasar ya amince da ƙarin albashi da kashi 114 wa kansa da mataimakinsa, gwamnoni da ma ma'aikata a ɓangaren shari'a. Tun farko, an ga rahoton da ya ce Hukumar Tarawa da Raba…
Read More
Ina goyon bayan sauye-sauyen da Gwamna Raɗɗa ke yi a Jihar Katsina – Masari

Ina goyon bayan sauye-sauyen da Gwamna Raɗɗa ke yi a Jihar Katsina – Masari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana ra'ayinsa akan salon kamun ludayin Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa. Masari ya bayyana ra'ayin na sa ne da yake jawabi a wurin wani taron liyafar cin abincin dare da Dattawan Jam'iyyar APC na jihar Katsina suka shirya domin karrama shi tare da yin addu'o'in samun nasara ga sabon Gwamnan da ta gudana a ɗakin taro na Paramount dake cikin birnin Katsina. A cewar Gwamna Masari, yana tare da Dikko Raɗɗa ɗari bisa ɗari kuma yana goyon bayan sauye-sauyen da yake yi domin inganta…
Read More
An yi kira ga sabbin jami’an hana fasa ƙwauri 335 da aka yaye a Kano su zama jakadu nagari

An yi kira ga sabbin jami’an hana fasa ƙwauri 335 da aka yaye a Kano su zama jakadu nagari

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kwalejin Horas da Jami'an Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa dake Gordon dutse a jihar Kano ta yaye sabbin jami'ai da suka kammala karvar horo guda 335. Taron wanda ya samu baquncin mataimakin kwanturola na qasa mai kula da sashin bincike, Muhammad Abba Kurra. Da yake jawabi mataimakin kwanturola janar na hukumar ya ce waɗanda aka yaye ɗin su zama jakadun hukumar a duk inda za a kaisu, aikinsu nagari zai ƙarawa hukumar daraja akasin haka kuma zai zubar musu da kima. Ya yi kira gare su akan su yi aiki da doka da ƙa'ida ta…
Read More
Sabbin Hafsoshin Soja: Janar-Janar 103 na fuskantar ritaya

Sabbin Hafsoshin Soja: Janar-Janar 103 na fuskantar ritaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Baya ga shirin ritayar da ake shirin yi, za a kara wa jami’ai da dama ƙarin girma zuwa matsayi na gaba don cike guraben da manyan hafsoshin da suka yi ritaya za su samar a wani vangare na sake tsara ayyukan da sabbin shugabannin ma’aikata ke yi. Hakan dai na faruwa ne watanni shida bayan da manyan hafsoshin soja 24 da birgediya-janar 38 suka yi ritaya a watan Disambar da ta gabata bayan shafe shekaru 35 suna hidimar ƙasar. Tinubu ya sanar da murabus ɗin Janar Lucky Irabor wanda shi ne babban hafsan tsaron…
Read More
N3m kacal na tarar a asusun Zamfara – Gwamna Dauda

N3m kacal na tarar a asusun Zamfara – Gwamna Dauda

'Da bashi nake gudanr da harkokin jihar' Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara,Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa, Naira miliyan uku kacal ya tarar a asusun jihar bayan da ya karɓi mulki ranar 29 ga mayu. Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a hirar da BBC Hausa ta yi da shi a ranar Litinin. Lawal ya ce gwamnatin da ya gada ta gaza biyan albashin ma'aikata na wata uku a jere kafin mulki ya dawo hannunsa. “Mummunan yanayi muka gada,” in ji Lawal. Ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin da ta gabata ta bar asusun jihar a bushe babu komai.…
Read More
Rusau a Kano: Ƙungiya ta yi barazanar maka Gwamna Abba a kotu

Rusau a Kano: Ƙungiya ta yi barazanar maka Gwamna Abba a kotu

Ta bai wa Gwamnan sa'o'i 72 ya janye aikin rusau da yake yi Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Good Governance and Change Initiative (GGCI), ta bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, wa'adin sa'o'i 72 a kan ya dakatar da rusau da yake yi a jihar sannan ya gayyato 'yan kasuwa da ɗaiɗaikun mutanen da lamarin ya shafa don warware matsalar cikin ruwan sanyi. Ƙungiyar ta yi barazanar maka Gwamnan a kotu muddin wa'adin da ta shata masa ya ƙare ba tare da yin abin da ya kamace shi ba. Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata…
Read More
Gwamnan Kano ya miƙa sunayen kwamishinoni ga majalisar jihar

Gwamnan Kano ya miƙa sunayen kwamishinoni ga majalisar jihar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane 19 da yake son ya naɗa a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwar jihar. A ranar Talata ce Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Honorabul Yusuf Falgore, ya karanto jerin sunayen da gwamnan ya aike wa majalisar. Waɗanda aka zaɓa ɗin dai za su hallara gobe Laraba da ƙarfe 10:00 na safe a gaban majalisar dokokin domin tantancewa. Ga jerin sunayen kamar haka: Comrade Aminu Abdulsalam Hon. Umar Doguwa Ali Haruna Makoda Hon. Abubakar Labaran Yusuf Hon. Danjuma Mahmoud Hon. Musa Shanono Hon. Abbas Sani Abbas Haj. Aisha…
Read More
Gwamnan Kaduna ya bai wa tsohon ma’aikacin Jaridar Blueprint muƙami

Gwamnan Kaduna ya bai wa tsohon ma’aikacin Jaridar Blueprint muƙami

Daga BASHIR ISAH Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya naɗa tsohon ma'aikacin Jaridar Blueprint, Samuel Aruwan, a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Birnin Kaduna (KCTA). Aruwan, wanda ya kasance Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna a baya-bayan nan, tsohon wakilin Jaridar Blueprint ne a jihar kafin daga bisani ya zama shugaban ofishin jaridar na Kaduna. Masanin aikin jarida ne wanda ke da ƙwarewar aiki na shekaru da dama inda a shekarar 2015 ya koma aiki da gwamnati. Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya fitar a ranar Talata yaba da ƙwarewar Aruwan…
Read More