N3m kacal na tarar a asusun Zamfara – Gwamna Dauda

‘Da bashi nake gudanr da harkokin jihar’

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Zamfara,Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa, Naira miliyan uku kacal ya tarar a asusun jihar bayan da ya karɓi mulki ranar 29 ga mayu.

Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a hirar da BBC Hausa ta yi da shi a ranar Litinin.

Lawal ya ce gwamnatin da ya gada ta gaza biyan albashin ma’aikata na wata uku a jere kafin mulki ya dawo hannunsa.

“Mummunan yanayi muka gada,” in ji Lawal.

Ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin da ta gabata ta bar asusun jihar a bushe babu komai. Muna aiki tuƙuru don bunƙasa yanayin, sai dai zai ɗauki lokaci.”

Kazalika, Gwamnan ya ce jihar ta gaza wajen biyan hukumomin tsaro alawus ɗinsu a wancan lokaci.

Ya ce ɗaliban makarantun sakandare a Zamfara ba su samu zarafin rubuta jarrabawar WAEC ko NECO ba a wancan lokaci.

“Da bashi nake gudanar da harkokin jihar tun da na karɓi ragamar mulkin Zamfara. Na tarar da asusun jihar babu kuɗi. Naira miliyan uku zuwa huɗu kawai ke ciki,” in ji Gwamnan.