Gwamnatin Kano ta fara bincike kan zaftare wa ma’aikata albashi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da cire Naira 370 na kowane wata daga albashi da fansho na ma’aikatan gwamnatin jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi a wata takarda da ya aike wa ɗaukacin shugabannin hukumomin a ranar Litinin wacce Manhaja ta gani a ranar Talata ta ce, an dakatar da cire kuɗaɗen nan take har sai an kammala bincike kan tsarin.

Gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ce ta ƙaddamar da wannan tsarin wanda ake zuba kuɗaɗen da aka cire a asusun wani kamfani mai suna Share Benefit Investment Limited.

Sakataren ya ƙara da cewa, sanarwar tana da muhimmanci sosai ga shugaban hukumomi da ma’aikatun gwamnatin don isar da sanarwar ga ɗaukacin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a cikin jihar.

Manhana ta rahoto cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin bincikar gwamnatin da ya gada.

Tuni dai, gwamnan ya fara rusa gine-ginen da ya ce haramtattu ne a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *