‘Yan bindiga sun kashe mutum uku a Kaduna

  • Sun yi garkuwa da wasu da dama

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga Jihar Kaduna sun ce, aƙalla mutum uku sun mutu yayin da aka yi garkuwa da wasu dama sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai garin Sabon Layi cikin yankin Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari da ke jihar.

Duk da dai ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a hukumance kan batun daga ɓangaren hukuma, sai dai wani jigo a yankin da lamarin ya faru, Anas Musa, ya tabbatar da aukuwar harin ga jaridar News Point Nigeria a ranar Juma’a.

A cewar Musa, ‘yan bindigar sun dira ƙauyen ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Alhamis inda suka yi harbe-harben bindiga barkatai wanda hakan ya yi ajalin wasu manoma uku a yankin.

Ya ce waɗanda lamarin ya shafa su ne: Anas Sabonlayi da Abubakar Dankibiya da kuma Harisu Un-Guwar Lemu.

Shugaban ƙungiyar Birnin Gwari Emirate Progressive Union (BEPU), Usman Kasai, shi ma ya tabbatar da aukuwar harin.

Da aka nemi jin ta bakin ‘yan sandan yankin, mai mgana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ya ba da tabbacin za a ji daga gare su bayan kammala tattara bayanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *