Shugaba Tinubu ya rushe hukumomin gudanarwa na ma’aikatun gwamnati

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da rushe duka hukumomin gudanarwa na ma’aikatu da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya haɗi da na kamfanoni mallakar gwamnatin.

Tinubu ya yi hakan ne domin sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora masa don amfanin al’umma.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Darktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar.

Sanarwar ta ce rushewar ta fara aiki ne nan take ba da ɓata lokaci ba.

“Sai dai rushewar ba ta shafi hukumomi da cibiyoyin da ke lissafe cikin Zubi na Uku, Kashi na 1, Sashe na 153 (i) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 na Tarayyar Nijeriya wanda aka yi wa gyaran fuska,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ya zuwa lokacin da za a kafa sabbin hukumomin gudanarwa na ma’aikatu da cibiyoyin da lamarin ya shafa, an buƙaci Manyan Jami’an ma’aikatun da su miƙa batutuwan da za su taso ga Fadar Shugaban Ƙasa ta hannun Manyan Sakatarorinsu.

Yayin da su kuma Manyan Sakatarorin za su miƙa batutuwan ga Shugaban Ƙasa ta hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya, in ji sanarwar.

Ta kuma buƙaci wuraren da lamarin ya shafa da su tabbatar da sun yi biyayya ga wannan umarni da ya fara aiki daga ranar Juma’a, 16 ga Yuni, 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *