Daga BASHIR ISAH
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tafi ziyarar aiki Paris, babban birnin ƙasar Faransa ya zuwa ranar Alhamis, 22 ga Yuni.
Wannan ita ce ziyara ta farko da Tinubu zai yi a matsayin Shugaban Ƙasa.
Tinubu zai yi ziyarar ce domin halartar taron shugabannin duniya inda za su rattaɓa hannu kan Sabuwar Dokar Kuɗi ta Duniya wadda za ta da ba da fifiko kan ƙasashe marasa ƙarfi wajen samun tallafi da zuba jari biyo bayan matsanancin sauyin yanayi da kuma bayan tasirin annobar Korona.
Taron wanda na yini biyu ne, zai gudana ne daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Yuni, zai kalli batun matsalar bashin da wasu ƙasashe ke fuskanta da kuma sauran matsalolin da ke yi wa cigaban ƙasa tarnaƙi.
Taron zai kuma kalli yadda za a farfaɗo da tattalin arzikin ƙasashe da ke fuskantar koma bayan tattalin arziki sakamakon tasirin annobar Korona, da kuma matsalar talaucin da ta addabar wasu ƙasashen duniya da zummar buɗa musu hanyoyin samun kuɗaɗe da zuba jari da zai taimaka musu wajen bunƙasa.