Tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya amsa gayyatar Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC).
A ranar Talata EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan don amsa mata tambayoyi kan abin da ya shafi zamanin mulkinsa.
Majiyarmu ta ce Ortom ya isa harabar ofishin hukumar da ke Makurdi ne da misalin ƙarfe 10:08 na safe.
Ƙarin bayani na tafe…