Layin lantarki na Shiroro-Kaduna ya lalace – KEDCO

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO, ya yi ƙarin haske dangane da ƙarancin wutar lantarki da ake fuskanta a jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa.

Kamfanin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi wadda shugaban sashen yaɗa labaran kamfanin, Sani Bala Sani, ya sanya ma hannu ta ce, lamarin ya faru ne sakamakon lalacewar layin wutar na Shiroro-Kaduna 330KV.

Kamfanin ya bayyana cewa tuni dai TCN ta fara aikin gyaran layin wutar wanda ake saran kammalawa a jiya lahadi.

Daga ƙarshe ya bai wa al’umma haƙuri tare da bada tabbacin cewa komai zai dai-daita da zaran aka kammala aikin gyaran.

Rahotanni sun nuna cewa tun a satin da ya gabata aka fara samun ƙarancin wutar lantarki a faɗin waɗannan jahohi lamarin da ya sanya al’umma cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi, musamman ta ɓangaren ruwan sha da kasuwanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *