Iyalan Nnamdi Kanu sun kori lauyoyinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Iyalan Shugaban Ƙungiyar Masu Fafutukar Kafa Ƙasar Biyafara (IPOB) da ake tsare da shi, Mazi Nnamdi Kanu, sun kori manyan lauyoyinsa, Mike Ozekhome, SAN; da Ifeanyi Ejiofor.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aanin Kanu, Kanunta Kanu, ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa na Tiwita a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2023.

Zargin ƙin amincewa da lauyoyin suka yi na barin likitocin Kanu na ƙashin kansa su same shi domin yi masa tiyatar gaggawa ne babban dalilan ɗaukar matakin.

Sanarwar mai taken ‘Sanarwar sallama’ a wani vangare tana cewa “Mik Ozekhome, SAN da lfeanyi Ejiofor yanzu ba a buƙatar ayyukansu a shari’ar Nnamdi Kanu da ke gaban Kotun Ƙolin Nijeriya da duk abin da ya shafe shi.

“Bayan ƙarar Mazi Nnamdi kanu a ranar 11 ga Mayu 2023 Farfesa Mike Ozekhome SAN ya ƙi ganin wanda yake karewa a hedikwatar DSS a Abuja ko da bayan saƙonni da dama daga wansa yake karewar na ganinsa.

“Iyalan Kanu sun yaba da lokacinku da ƙoƙarinku ya zuwa yanzu, don Allah ku miƙa takardun doka da gaggawa,” iyalan suka ambata a cikin takardar sallamar.”