Umarnin Kotu: Ba mu hana Emefiele ganin iyali da lauyoyinsa ba – DSS

Daga BASHIR ISAH

Hukumar tsaro ta DSS ta ce, an bai wa tsohon Gwmnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, damar ganin iyalinsa d likitocinsa tun kafin umarnin kotu a kan haka.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa DSS umarni kan ta ƙyale Emefiele ya gana da iyalai da kuma lauyoyinsa.

Sai dai cikin sanarwar da ta fitar ranar Asabar ta bakin kakakinta, Peter Afunanya, DSS ta ce ta rigaya ta bai wa tsohon Gwamnan na CBN damar ganawa da lauyoyin nasa tun kafin kotu ta ba da umarni.

Sanarwar ta ƙara da cewa, DSS na yin abin da ya dace wajen kula da sha’anin bincike da kuma duk wani da ake zargi da ke ƙarƙashin kulawarta.

“Kuma tana aiki da ƙwarewa da martaba doka daidai da tsarin mulkin dimokuraɗiyya,” in ji sanarwar.

DSS ta kuma gargaɗi masu take-taken yaƙi da binciken da ake yi wa Mr Godwin Emefiele.