Sanusi ya yi ganawar sirri da Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A jiya Alhamis ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Sarkin Kano na 14 kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi (Khalifa Muhammadu Sanusi II), a fadar Aso Rock.

Ziyarar ta Sanusi, wadda ita ce ta farko tun bayan da shugaban ƙasar ya hau karagar mulki, na zuwa ne mako guda bayan da shugaban ƙasar ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN.

Ba a tantance tattaunawar da suka a wannan ganawa ta sirri ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Sanusi ya riƙe muƙamin shugaban CBN daga watan Yunin 2009 zuwa watan Yunin 2014 lokacin da Emefiele ya karɓi mulki daga hannun sa.

A ranar Juma’a ne shugaban ƙasar ya dakatar da Emefiele a matsayin shugaban babban bankin sannan kuma ya umurci mataimakin gwamnan ayyuka na bankin, Folashodun Shonubi, ya koma ofishinsa a matsayin mukaddashi.

Tun a ranar Asabar ɗin da ta gabata ne Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta tabbatar da cewa Emefiele yana hannunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *