Sarkin Musulmi ya bayyana ranar Babbar Sallah

Daga BASHIR ISAH

Ranar 28 ga watan Yuni idan Allah Ya kai mu take Babbar Sallah (Idil Kabir) ta bana.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III ne ya bayyana haka ranar Lahadi da daddare biyo bayan ganin jinjirin watan Zul-Hajja.

Sarkin Musulmi ya ce sakamakon ganin jinjirin watan, ya tabbata yau (Litinin) 1 ga Zul-Hijja na shekarar 1444 wanda ya yi daidai da 19 ga Yunin 2023.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Shugaban Kwamitin Bada Shawara na Fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya rattaɓa wa hannu a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, “Kwamitin Bada Shawara na Fadar Sarkin Musulmi Kan Sh’anin Addini tare da haɗin gwiwar Kwamitin Neman Wata na Ƙasa, sun samu rahoton ganin jinjirin watan Zul-Hajji na 1444 a ranar Lahadi.

“Sarkin Musulmi ya yarda da rahoton, don haka ya ayyana Litinin, 19 ga Yuni a matsayin 1 ga Zul-Hijja, 1442AH,” in ji sanarwar.

Zul-Hijja shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci, wanda a cikinsa ake aikin Hajji da kuma bikin Babbar Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *