Zuwa ga Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero

Assalam alaikum. Bayan sallama da gaisuwa irin wacce a kan yi wa ma’abota kwanciyar kushewa, da fatan Allah ya juya kafaɗarka ya Rahamsheka.

Dalilin rubuto maka wannan wasiƙa ita ce domin yin addu’a gareka da ambaton wasu kyawawan ayyukan da ka yi a lokacin rayuwarka wacce har ya zuwa yau muka kasa mantawa da kai, idanuwanmu ba su dai na zubar da hawaye ba, kuma tabon raunin da muka samu a sanadiyyar rashinka ya kasa warkewa.

Allahu Akbar! Kwanci-tashi babu wuya, kamar jiya kabar doron duniyar nan, amma gashi muna ƙidaya shekaru tara cif-cif da rasuwarka.

Ina son sanar da kai cewa, irin abubuwan alheri da ka yi na raya addini kamar gina makarantu da Masallatai da sada zumunci da tausaya wa talakawa, har yanzu muna nan muna cin moriyarsu. Ko da yake an rasa waɗanda za su ɗora daga inda ka bari.

Jihadin nan da ka yi na hana gina Katafaren Coci a Jami’ar Tarayya ta jihar Kano har yanzu yana tasiri, domin kuwa har yanzu ba a sake tada zancen ba.

Tsawon zamani da kayi a mulkinka cikin rungumar ‘yan Kano gaba ɗaya a matsayin ‘ya’yanka ba tare da nuna bambanci ba, tare da haɗa kan malaman addini su zauna lafiya duk da irin bambance-bambancen da ke a tsakaninsu ita ce ta zama tarihi a yau, don ta zama fam-fam-fam inji yara.

Allah ya kai haske kabarinka, tun ranar da kabar gidan duniya, aka naxa magajinka irin waccen nagartar tayi vatan dabo daga farfajiyar Masarautar domin al’amarin mu kanmu ya ɗaure mana kai, a ce irin kyakkyawar shimfiɗar da ka bari ta bika kushewa.

Wasu na ganin cewa, tun radda aka tsittsinka masarautar taka gida huɗu, to daga rannan aka dasa wata itaciyar fitina a tsakanin ‘ya’yanka aka fara yi wa juna kallon hadarin kaji, aka kasa ci gaba da ɗora bulon ginin ayyukan alherin da ka bari aka koma zargin juna saboda Sarauta.

Allah ya kai haske kabarinka, ba don gudun kada a ce na cika tsegumi ba, da na ce maka a yau masarautarka ta Jihar Kano, ta zama dandalin rikicin Malaman addini masu bambancin fahimta, domin kuwa a yanzu mumbarorin masallatan Juma’a da ka sani a da suna huɗubobin samar da haɗin kai da zaman lafiya, a yau sun koma wajen mayar da martani ga juna.

Allah ya rahamsheka, wai ka ko san daga rasuwarka zuwa yau Sarakuna nawa aka yi a Masarautarka? Uhmm, to a yanzu haka Sarakuna biyu suka yi Sarauta a cikin ‘ya’yanka, ko kasan dalili? Ka gafarce ni, domin kuwa faɗa maka dalilin zai iya vata maka rai.

A gaskiyar magana, dalilan ba su wuce irin abin da kayi ta ƙoƙarin hana faruwarsa ba a lokacin da kake raye, na sanin ka da kayi cewa, surka sha’anin Sarauta da siyasa tamkar gaurawa nono da kananzir ne waɗanda idan auka gaurawa sun fi ƙarfin sha sai dai zubarwa, domin abubuwa ne da kowannen sa ke zaman kansa, haɗa su biyu kuwa a lokaci guda na iya haifar da matsala, to a gaskiyar lamari, ramin da suka afka kenan, su kuma ‘yan siyasar ke ta wasan kura da su.

Allah ya kai haske cikin kushewarka, a yanzu maganar nan da nake da kai ana raɗe-raɗin kara sauya fasalin masarautar taka daga waccan tsohon tsari ta ‘yan huɗu, ko nawa za a mai da ita? Allah ne masani.

Sa’annan kuma, ana gab da mai da masarautar taka a tsarin ‘Sabon Sarki, sabon gwamna’, kaji kamar wasan yara.

Abubuwa ne fa masu tarin yawa suka faru kuma suke kan faruwa marasa daɗin ji, waɗannan ma da na ɗan tsegunta maka zazzaɓa na yi saboda taushinsu, amma akwai waɗanda baza su faɗu ba ga mutum iri na.

Af! na manta, ka tuna da katafariyar gonar nan taka ta gaba da Ƙauyen Sallari? Uhmm, bari dai in yi shiru kada a ce na cika tsegumi.

Daga ƙarshe, ina shaida maka cewa, gaskiyar magana ‘yan siyasa sun tsaga sun ga jini a cikin fadarka, don haka abubuwa sai wadda aka gani kawai, Allah ya kyauta.

Allah ya jiƙanka da rahama. Allah ya kyauta kwanciyarka. Allah ya ƙara haɗa kan ‘ya’yanka su dawo su rungumi irin tsohon tsarin da kafa ya wanzu har ya jawo wa masarautar darajar da aka rasa masu kamo ta a cikin sauran Masarautu.

Wassalam, sai kun qara ji na. Naku a kodayaushe.

Sani Shehu Lere, 08062798146.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *