CBN ya amince da bai wa ’yan canji damar sayen Dala 150,000 duk mako

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD 

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince da bai wa ’yan kasuwar canji (BDC) masu lasisi damar shiga Kasuwar Canjin Kuɗi ta Nijeriya (NFEM), inda kowanne ɗan canji zai riƙa sayen dala har 150,000 a kowane mako domin ƙara wadatar kuɗin waje da daidaita kasuwar ƙananan saye da sayarwa.

Umarnin ya fito ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 10 ga Fabrairu, 2026, wadda Daraktan Sashen Kasuwanci da Canji, Dakta Musa Nakorji, ya sanya wa hannu, inda aka aika da ita ga bankunan dillalai da kuma jama’a.

CBN ya ce, matakin na da nufin tabbatar da wadatar kuzin waje a ɓangaren ƙananan kasuwa domin biyan buƙatun masu amfani na gaskiya. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tazarar farashin dala tsakanin kasuwar gwamnati da ta bayan fage ta wuce N90 karon farko cikin shekaru uku.

Masana kasuwa na ganin cewa wannan mataki zai rage matsin lambar hasashe a kasuwar bayan fage tare da rage bambancin farashi ta hanyar ƙara hanyoyin da ake samun dala ta halal.

Sai dai bankin ya kafa ƙa’idoji masu tsauri. Bankunan dillalai dole su cika dukkan sharuɗɗan sanin abokin hulɗa (KYC) da binciken kwastomomi kafin su sayar wa ’yan canji da dala. Bayan kammala hakan, za a ba su damar saye bisa ƙa’idojin da ke akwai, amma kada su wuce iyakar dala 150,000 a mako.

Haka kuma, an umurci ‘yan canji su riƙa gabatar da rahotanni na lantarki cikin lokaci ga CBN. Bankin ya gargaɗi cewa ba za a yarda ‘yan canji su riƙe dala ba tare da amfani da ita ba; duk wata dala da ba a yi amfani da ita ba dole ne a sayar da ita cikin sa’o’i 24.

An kuma ƙarfafa dokar cewa, duk wata mu’amalar canji dole ta gudana ta asusun banki na gwamnati da hana hulɗar ɓangare na uku. An taƙaita mu’amalar kudi a hannu zuwa kashi 25 cikin ɗari kacal na kowace ma’amala.

Wannan mataki ya zo ne bayan takunkumin da aka sanya wa ‘yan canji a baya, inda aka rage musu damar sayen Dala daga bankuna. Sabuwar dokar ta Dala 150,000 a mako na nuna yunƙurin CBN na samar da daidaito tsakanin buɗe kasuwa da kuma tsaurara sa ido.

By ukarofi