Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (NRS), wadda a baya ake kira FIRS, ta karya tarihin shigar kuɗaɗen haraji da ba a taɓa samu ba inda ta tara Naira tiriliyan 28.3 a shekarar 2025, ta wuce hasashen tiriliyan N25.2 da aka gindaya mata da kashi 12 cikin ɗari.
An bayyana hakan ne a madadin Shugaban Hukumar, Zacch Adedeji, ta bakin Daraktar Zartarwa mai kula da Harkokin Gwamnati da Manyan Masu Biyan Haraji, Amina Ado Kurawa, a taron bita na kwana biyu da aka fara a Abuja mai taken “Designed to Adapt, Built to Deliver”.
A cewarta, an ɗora wa hukumar sabon burin tara Naira tiriliyan 40.71 a shekarar 2026, wanda ya fi na 2025 da kashi 44 cikin ɗari.
Yayin da yake jawabi, shugaban hukumar ya buƙaci ma’aikata su guji tsofaffin tunani da ka iya zama cikas ga ci gaba, yana mai cewa martabar tsarin haraji na Nijeriya da amincewar tattalin arzikin ƙasa na hannunsu.
Ya jaddada cewa nasarar shugabanci ba wai rashin ilimi ko ƙwarewa ke hana ta ba, sai dai wasu ɓoyayyun tunani da ke tasiri kan yanke shawara.
Dangane da rarrabuwar kuɗaɗen shiga na 2025, Amina Kurawa ta ce harajin da ba na man fetur ba ya kai tiriliyan N21.5, ya wuce tiriliyan N15.9 da aka samu a 2024 da kashi 35 cikin ɗari.
Harajin mai kuwa ya kai tiriliyan N6.6, wanda ya nuna ƙaruwa da kashi 19 cikin ɗari idan aka kwatanta da tiriliyan N5.8 na shekarar da ta gabata.
Ta ce, wannan ci gaba ya samo asali ne daga inganta tsarin gudanarwa, faɗaɗa tsarin riƙon haraji (Withholding), ƙara amfani da fasahar zamani, da kuma tsaurara matakan bin doka.
An kuma bayyana cewa warin burin da aka ɗora wa hukumar ya danganci faɗaɗa aikinta, ciki har da karɓar wasu kuɗaɗen shiga kamar kuɗin sarauta (royalty) da a baya Hukumar NUPRC ke karɓa.
Ministan Kuɗi kuma Mai Daidaita Tattalin Arziki, Wale Edun, wanda ya halarci taron ta kafar intanet, ya ƙarfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwar sayen kayayyakin cikin gida domin ƙarfafa tattalin arziki da kuma taimakawa wajen cimma burin haraji.
Shi ma Shugaban Kwamitin Aiwatar da Manufofin Haraji na ƙasa, Joseph Tegbe, ya jaddada cewa ingantaccen aiwatar da dokokin haraji ne zai tabbatar da nasarar sauye-sauyen da ake yi.
