Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Bagudu, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun haifar da ƙarin kuɗaɗen shiga ga jihohi da ƙananan hukumomi, lamarin da ya ba su damar samar da ƙarin ayyukan more rayuwa ga al’ummominsu.
Ministan ya bayyana haka ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa (NEC) wanda aka kammala a ranar Talata a Abuja, inda ya kuma yaba wa shugaban ƙasa kan yadda ya ƙarfafa tsarin tarayya a Nijeriya. Ya ce, “Shugaba Tinubu ya ƙarfafa tsarin tarayyar mu.”
Bagudu ya jaddada cewa goyon bayan da shugaban ƙasa ke bai wa Majalisar Tattalim Arzkki (NEC) — wadda ta ƙunshi gwamnonin jihohi 36 da Ministan Babban Birnin Tarayya — ya taimaka matuƙa wajen inganta haɗin kai tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa, sha’awar da Shugaba Tinubu ke nunawa majalisar, wadda ke zama mai ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki, na nuna cikakken imaninsa da haɗin kan tsarin tarayya. A cewarsa, yadda shugaban ke tafiyar da harkokin mulki ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba ya rage saɓanin da kan haddasa tsaiko tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.
Yana bayyana misali, Bagudu ya ce a cikin majalisar NEC ana bai wa gwamnonin jihohi damar bada gudunmawa kan mafi yawan sauye-sauyen da ake aiwatarwa, kuma abin a yaba ne yadda yawancinsu — ba tare da la’akari da jam’iyya ba — ke ganin shugaban ƙasa na bin hanyar da ta dace ga ƙasa tare da mara wa gwamnatin tarayya baya. Har ma wasu daga cikinsu sun ce ba za su iya kare kasancewarsu a wata jam’iyya ta daban ba.
Dangane da ribar da aka samu a zahiri, ministan ya ce halin kuɗaɗen shiga na jihohi da ƙananan hukumomi ya inganta, inda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta ɗauki mafi yawan nauyin sauye-sauyen.
Bagudu ya kuma ja hankalin mahalarta taron kan yadda shugaban ƙasa ke bai wa matakan gwamnati na ƙasa da su fifiko, yana mai cewa hakan na nuna imaninsa cewa ainihin tsarin tarayya na gaskiya shi ne wanda ke gane ƙarfin da ke tattare a matakin gwamnati mafi kusa da jama’a, tare da tallafa wa samar da arziki mai ɗorewa a can.
Ya ce, hakan ne ya sa Shugaba Tinubu ya amince da shirin “Renewed Hope Ward-based Development Programme”, wanda ke da nufin gano ayyukan tattalin arziki a mazaɓu 8,809 na ƙasar nan tare da tallafa wa bunkasarsu.
Bagudu ya taya shugaban ƙasa murna kan yadda sauye-sauyen tattalin arzikinsa masu ƙarfi da jajircewa ke samun karɓuwa a duniya baki ɗaya.
A cewarsa, “A makon jiya kawai, wata tawagar Bankin Duniya da ta ziyarci ƙasar nan, ƙarƙashin jagorancin Daraktan Ayyuka, ta bayyana wa duniya cewa sauye-sauyen Nijeriya sun zama abin koyi a duniya.”
Ya ƙara da cewa, rahoton Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da ya rufe wannan lokaci ya sanya Nijeriya cikin ƙasashe goma na gaba da ke bada gagarumar gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, baya ga sauran kalamai daga shugabannin ƙasashe, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma masu zaman kansu.
Taron NEC mai taken “Isar da Ci Gaba Mai Haɗa Kowa da Ci Gaba Mai ɗorewa: Tsarin Ci Gaban ƙasa na Shirin Renewed Hope 2026–2030” shi ne karo na biyu cikin shekaru goma, kuma Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya jagorance shi, wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Tattalin Arziki.
