CAC a shekara 35: Mun soke rajistar kamfanoni 400,000 a 2025 – Magaji

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Nijeriya (CAC), ta sanar da cewa ta soke rajistar kamfanoni fiye da 400,000 da ba sa aiki a shekarar 2025.

Wannan mataki, a cewar shugabannin hukumar, wani ɓangare ne na babban garambawul da nufin tsaftace tsarin kasuwanci, kare tattalin arziki, da kuma dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari a cikin gida da waje.

Magatakarda-Janar na hukumar, Hussaini Magaji, SAN, ne ya bayyana haka a Abuja yayin wani tattakin motsa jiki da aka shirya domin bikin cikar CAC shekaru 35 da kafuwa.

Ya ce yawancin kamfanonin da aka soke rajistarsu sun daɗe ba sa gudanar da aiki, kuma sun gaza cika wajibcin shigar da rahoton shekara-shekara kamar yadda doka ta tanada.

A cewarsa, barin irin wadannan kamfanoni a rajista na gurgunta amincewa da tsarin kasuwancin Nuujeriya, tare da buɗe ƙofar yin amfani da sunan kamfani wajen aikata zamba da sauran laifukan tattalin arziki.

“Tsaftace rajista wajibi ne domin tabbatar da cewa tsarin kasuwancinmu abin dogaro ne,” inji shi.

Magaji ya jaddada cewa sahihin rajista mai gaskiya da tsari shi ne ginshiƙin jawo jarin waje, tare da hana amfani da tsarin kamfani wajen ɓoye haramtattun ayyuka.

Ya ƙara da cewa, daga ofis guda a Garki lokacin kafuwarta ƙarƙashin dokar Companies and Allied Matters Act, CAC ta rikiɗe zuwa cikakkiyar hukuma mai bayar da hidima ta zamani, bayan gyaran dokar Companies and Allied Matters Act da ya sabunta ayyukanta.

A yau, a cewarsa, ayyukan rajista da sarrafa kamfani ana yi su gaba ɗaya ta yanar gizo, sa’o’i 24 a rana. Wannan sauyi ya taimaka matuka wajen saukaka harkokin kasuwanci, inda ‘yan kasuwa za su iya rajista ko gyara bayanai ba tare da zuwa ofis ba.

Hukumar ta kuma haɗa gwiwa da Small and Medium Enterprises Deɓelopment Agency of Nigeria domin rajistar ƙanana da matsakaitan sana’o’i 250,000 kyauta a 2025, tare da basu horo da tallafin inganta kwarewa.

Shugaban CAC ya ce an samu ci gaba a jin daɗin ma’aikata da tsarin aikinsu, lamarin da ya ƙara inganta hidima. Bikin tattakin ya zama wata alama ta ƙarfi, haɗin kai da juriyar hukuma bayan shekaru 35 na aiki a fagen rajista da tsare-tsaren kasuwanci.

By ukarofi