JAMB ta ƙaryata batun tsawaita rijistar jarrabawar UTME ta 2026

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB), ta bayyana ƙarara cewa za ta rufe rijistar Jarrabawar Shiga Jami’o’i ta 2026 (UTME) a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026, tare da jaddada cewa babu wani shiri na tsawaita wa’adin.

Hukumar ta yi wannan bayani ne a cikin sanarwarta ta mako-mako da ta fitar a ranar Litinin, inda ta buƙaci dukkan masu niyyar rubuta jarrabawar su gaggauta kammala rijistarsu ba tare da jira zai lokaci ya ƙure ba.

JAMB ta nuna damuwa kan yadda cibiyoyin rijista da dama ke fuskantar ƙarancin masu zuwa yin rijista a wannan mataki, duk da cewa wa’adin ya rage kwana 17 kacal.

A cewar hukumar, al’adar da ta saba maimaituwa ta jinkirta rijista har zuwa kwanaki na ƙarshe, sannan a fara neman a ƙara lokaci, ba za ta samu karɓuwa ba a shekara ta 2026.

“Wannan ɗabi’a ta jinkirta yin rijista da gangan, sannan daga bisani a fara neman tsawaita wa’adi, ba za a lamunce da ita ba a bana,” inji hukumar.

Ta ƙara da cewa, tana sane da wasu dabaru da ake zargin masu satar jarabawa da wasu da ke fakewa da sunan masu cibiyoyin koyarwa ke amfani da su, inda suke ba ɗalibai shawarar su dakata su jira ƙarshe.

A cewar JAMB, ana yin hakan ne domin tilasta a tsawaita wa’adin rijista, wanda hakan kan bai wa wasu damar haɗa ɗalibai gungu-gungu zuwa wasu cibiyoyi, lamarin da ka iya sauƙaƙa aikata maguɗin jarrabawa.

Hukumar ta tunatar da cewa rijistar UTME ta 2026 ta fara ne a ranar 26 ga Janairu, kuma an tsara ta ne ta ɗauki tsawon makonni biyar, ba tare da wani sauyi a jadawalin ba.

Ta kuma bayyana cewa kimanin ɗalibai miliyan ɗaya sun riga sun nuna sha’awar rubuta jarabawar, yayin da da dama suka sayi lambar ePIN, kuma ake sa ran su kammala rijista cikin gaggawa.

JAMB ta ce, tsawaita wa’adin ba abu ne mai yiwuwa ba, domin jaddawalinta ya dace da na sauran hukumomin shirya jarrabawa a faɗin ƙasa.

“Duk wani ƙarin lokaci zai kawo cikas ga tsare-tsaren da aka tsara tare da sauran jarrabawar ƙasa, tare da mamaye lokacin da aka ware musu,” inji hukumar.

Saboda haka, ta bukaci ɗalibai da su yi rijista cikin lokaci, su guji cunkoso na ƙarshe, kuma su yi watsi da duk wata jita-jita da ke cewa za a ƙara wa’adin.

Hukumar ta nanata cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani ɗalibin da ya kasa yin rijista cikin wa’adin da aka gindaya ba.

By ukarofi