CBN zai sauya tsarin wasu takardun kuɗin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, nan ba da daɗewa ba zai sake tsarin wasu takardun kuɗin Nijeriya.

Bankin ya ce takardun da sake tsarin zai shafa sun haɗa da N200 da N500 da kuma N1,000.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai ran Laraba a Abuja.

Emefiele ya ce, ya zuwa 15 ga Disamban wannan shekarar za a fara amfani da takardun kuɗin da aka sake wa tsarin.

A cewar Emefiele, Gwamnatin Tarayya ce ta buƙaci CBN da ya duba ya sake tsarin takardun kuɗin da lamarin ya shafa.