Kotu ta umarci Nijeriya ta biya Kanu diyyar miliyan N500

Daga BASHIR ISAH

Wata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Umuahia, babban birnin jihar Abia, ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ta maida shi Kenya inda ta kamo shi a ranar 19 ga Yunin 2021.

Haka nan, kotun ta kuma buƙaci gwamnatin ta biya Kanu kuɗi miliyan N500 a matsayin diyyar kamo shi daga Kenya da ta yi ba bisa ƙa’ida ba.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a E.N Anyadike, ya jaddada cewa kama Kanu ba bisa ƙa’ida ba da gwamnatin ta yi take haƙƙinsa na ‘yanci ɗan Adam ne.

Ya ce, gwamnatin ta kasa kare kanta dangane da ƙorafin da Kanu ya yi cewa an kama shi, an ɗaure shi da kaca na tsawon kwana takwas, an kuma gana masa azaba kafin kawo shi Nijeriya.